An tsinci gawawwakin mahauta 2 cikin 3 da aka yi garkuwa da su a garin Ala

An tsinci gawawwakin mahauta 2 cikin 3 da aka yi garkuwa da su a garin Ala

  • An tsinci gawawwaki 2 cikin mahauta 3 da aka yi garkuwa da su a garin Ala da ke karamar hukumar Akure ta arewa a jihar Ondo a cikin daji
  • An yaudari mahauta 4 mazauna Akure, babban birnin jihar zuwa cikin surkukin daji da sunan tallata mu su shanaye idan za su siya
  • Nasiru Jamilu, daya daga cikin mahautan da ya tsira ya bayyana yadda lamarin mai furgitarwa, inda ya ce sun saba da siyan shanu wurin mutanen

Jihar Ondo - An tsinci gawawwaki 2 cikin mahauta 3 da aka yi garkuwa da su a garin Ala da ke karamar hukumar Akure ta arewa a jihar Ondo cikin daji, Daily Trust ta ruwaito.

Am samu bayanai akan yadda aka yaudari wasu mahauta 4 cikin daji da sunan za a sayar mu su da shanu.

Kara karanta wannan

Borno: Arangama ta da 'yan ta'addan ISWAP a kan titi, Malamin makaranta

An tsinci gawawwakin mahauta 2 cikin 3 da aka yi garkuwa da su a garin Ala
An tsinci gawawwakin mahauta 2 cikin 3 da aka yi garkuwa da su a garin Ala, jihar Ondo. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Daily Trust ta bayyana yadda Nasiru Jamilu, daya daga cikin mahautan da ya tsira ya bayar da bayani akan yadda lamarin ya auku, inda ya ce:

“Mutanen sun saba sayar wa mai gidanmu shanu don haka su ka bukaci mu bisu daji don siyan wasu shanu. Duk da dai mun dade rabon da muyi siyayya a wurinsu.
“Mun kama hanyar zuwa wurinsu ranar Asabar amma wurin ya yi mana nisa. Mai gidanmu ya bukaci mu dawo don ba ya jin zuwa. Daga nan mutumin ya dame shi inda ya ce za su kawo shanun kusa.
“Bayan ya kara kira ne ya sanar damu cewa akwai wasu mutanen da zamu hadu da su a garin Ala kafin su kai mu wurin shanun.”

Kara karanta wannan

Innalillahi: Miyagun yan bindiga sun bude wa mutane wuta ana tsaka da jana'iza a Benuwai

Sai da su ka shiga daji su ka fito da bindigogi

Ya labarta yadda su ka kai su wurin shanun sannan su ka bukaci su ajiye ababen hawan su sannan su kora shanu zuwa titi.

Bayan sun shiga cikin dajin ne su ka ciro bindigogi su ka fara harbin iska, anan su ka yi garkuwa da babban mahaucin.

Ya kara bayyana yadda su ka yi kokarin tserewa daga nan Jamiu ya fadi kasa kamar ya mutu, bayan ya tabbatar sun tafi ya mike ya tsere.

Yanzu haka Jamilu ya na asibitin Akure ana kulawa da lafiyarsa, inda ya ce tabbas garkuwa aka yi da mai gidansu amma bai tabbatar da halin da sauran biyun su ke ciki ba.

Sai dai ‘yan sanda sun tsinci gawawwakin sauran biyun.

Kakakin rundunar ‘yan sandan yankin, Mrs Funmilayo Odunlami, ta ce su na iyakar kokarin ganin sun ceto dayan mahaucin da ke hannun ‘yan bindigan.

Kara karanta wannan

Borno: Dan majalisa a ya bayyana yadda 'yan ISWAP suka kone gidan da ya ginawa dan uwansa

'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe

A wani labarin, 'yan sanda sun yi ram da samari 2 bisa kama su dumu-dumu da laifin sare wa juna hannaye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

An ruwaito yadda ‘yan sandan su ka kama Adamu Mohammed da Bukar Audu, bayan sun datse wa juna hannaye yayin wani fada da su ka tafka a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe.

Premium Times ta bayyana yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, a ranar Litinin a Damaturu ya bayyana a wata takarda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel