Ana tsaka da zaman makoki, Miyagun yan bindiga sun bude wa mutane wuta a Benuwai

Ana tsaka da zaman makoki, Miyagun yan bindiga sun bude wa mutane wuta a Benuwai

  • Wasu yan bindiga da ba'a san su ba sun buɗe wa mutane wuta yayin da suke shirin gudanar da jana'iza a jihar Benuwai
  • Rahoto ya bayyana cewa maharan sun bindige aƙalla mutum 4 har lahira, yayin da wasu da dama suka jikkata
  • Shugaban ƙaramar hukumar Logo, Terseer Agber ya tabbatar da lamarin da cewa ya shaida wa DPO na yankin kan harin

Benue - Tsagerun yan bindiga sun kashe mutanen dake shirin jana'iza aƙalla 4 a ƙauyen Mbayato ƙaramar hukumar Logo, jihar Benuwai.

The Nation ta ruwaito cewa lamarin ya faru da sanyin safiyar ranar Asabar, yayin da yan uwa da abokan arziki suke shirin gudanar da jana'izar wata mata a Mbayato.

Wani shaidan gani da ido, Kundushima Acka, ya shaida wa manema labarai cewa maharan sun zo da yawansu da misalin karfe 4:00 na safe, inda suka bude wa mutanen wuta kan mai uwa da wabi.

Kara karanta wannan

Zamfara: Ƴan bindiga sun yi wa dagaci yankan rago a gaban jama'a, kun kashe wasu 8

Jihar Benuwai
Ana tsaka da zaman makoki, Miyagun yan bindiga sun bude wa mutane wuta a Benuwai Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Acka ya kara da cewa mutum hudu suka mutu, yayin da wasu da dama aka garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu bayan samun raunuka a harin.

Meyasa suka kai wannan hari?

A cewar mutumin, shugaban sabbin jami'an sa kai na yankin, (CVG), yana daga cikin mutunen da aka bindige a harin.

Bugu da ƙari, Acka ya yi zargin wannan mummunan harin ya na da alaƙa da matsin lambar da jami'an CVG suka yi wa yan bindiga kwanan nan.

Kakakin yan sandan jihar, Kate Anene, ba ta ɗauki kiran wayan salula da aka mata ba, haka kuma ba ta turo amsar sakon karta kwana da aka tura mata ba.

Shin mahukunta sun san da lamarin?

Shugaban ƙaramar hukumar Logo, Terseer Agber, ya tabbatar da rahoton kai harin, kuma yace tuni ya kaiwa DPO rahoton faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun bindige wani mai garkuwa da mutane da yayi kokarin tserewa a jihar Niger

Ba da jimawa da gwamanan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya sa hannun kan dokar yan bijilanti da aka yi wa garambawul.

Ya yi kira ga waɗan da aka naɗa a matsayin jami'an CVG su kawo ƙarshen aikata ta'addanci a faɗin jihar, kamar yadda Tribune ta rahoto.

A wani labarin kuma Sojoji sun hallaka mayakan Boko Haram/ISWAP da yawa a wani kwantan bauna a jahar Borno

Dakarun sojin Operation Hadin Kai (OPHK) na bataliyar ta 82 sun yi wa mayakan ISWAP/Boko Haram mummunan ɓarna a yankun Pulka, jihar Borno.

Sojojin sun samu wannan nasara ne tare da taimakon jami'an sakai na JTF, da yan bijilanti bayan samun bayanan sirri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel