Gwarazan yan sanda sun fatattaki tsagerun yan bindiga, sun ceto mutane da dabbobi a jihar Katsina

Gwarazan yan sanda sun fatattaki tsagerun yan bindiga, sun ceto mutane da dabbobi a jihar Katsina

  • Rundunar yan sanda reshen jihar Katsina ta dakile harin wasu tsagerun yan bindiga a Gidan Duka, karamar hukumar Kankara
  • Kakakin yan sandan jihar, Gambo Isah, shine ya sanar da haka, yace an kuma kwato shanu da tumaki da dama a hannun su
  • Hukumar yan sandan ta kuma sanar da samun nasarar ceto wasu mutum 11 da yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin Safana

Katsina - Gwarazan jami'an yan sanda sun dakile harin yan bindiga a kauyen Gidan Duka, karamar hukumar Kankara, a jihar Katsina.

Premium Times ta rahoto cewa yan sanda sun kuma samu nasarar kwato shanu 38 da kuma tumaki 11 daga hannun maharan.

Kakakin yan sandan jihar, Gambo Isa, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, yace yan bindigan sun kwashi kashin su a hannun tawagar yan sanda bisa jagorancin DPO na yankin.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan sanda sun ceto tsoho mai shekaru 80 daga hannun masu garkuwa da mutane

Yan sanda a bakin aiki
Gwarazan yan sanda sun fatattaki tsagerun yan bindiga, sun ceto mutane da dabbobi a jihar Katsina Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Isah yace:

"Tawagar yan sandan sun tari yan bindigan a dai-dai ƙauyen Danramabu, inda suka yi musayar wuta tsakaninsu."
"Yan bindigan sun tsere cikin jeji suka bar dabbobin da suka sato, wanda ya haɗa da shanu 38 da tumaki 11."
"Jami'an sun kuma kwato mashin Bajaj mallakin yan bindigan yayin musayar wuta."

An ceto mutum 11 da akayi garkuwa da su

Kakakin yan sandan ya bayyana cewa jami'an sun samu nasarar ceto mutum 11, ranar Lahadi da safe, waɗan da aka sace a Sabon Garin Safana.

Mista Isa yace jami'ai sun ceto mutanen ne a maɓoyar yan bindiga dake kauyen Tsatskiya, ƙaramar hukumar Safana.

A cewarsa yanzun haka an kai mutanen da aka ceto babban Asibitin Dutsin-Ma domin duba lafiyarsu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Miyagun yan bindiga sun bude wa mutane wuta ana tsaka da jana'iza a Benuwai

Rahoto ya nuna cewa yan bindigan sun yi garkuwa da mutanen ne tun watan Nuwamban shekarar da ta gabata, kuma sun rike su har tsawon wannan lokacin.

A wani labarin kuma Sojojin Najeriya sun hallaka kasurgumin kwamandan yan ta'adda da wasu 37 a Askira, jahar Borno

Rahoto ya nuna cewa sojojin sun shirya sun sake farmakan yan ta'addan domin ɗaukar fansa kan kisan manyan sojoji.

Mazauna garin Askira Uba sun yaba da yadda dakarun sojin suka ɗauki matakin gaggawa yayin da yan ISWAP suka shigo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel