Harin Fansa: Sojojin Najeriya sun hallaka kasurgumin kwamandan yan ta'adda da wasu 37 a Askira

Harin Fansa: Sojojin Najeriya sun hallaka kasurgumin kwamandan yan ta'adda da wasu 37 a Askira

  • Dakarun sojin Najeriya sun kashe babban kwamandan yan ta'addan ISWAP da wasu mambobinsa da dama a Askira Uba, jihar Borno
  • Rahoto ya nuna cewa sojojin sun shirya sun sake farmakan yan ta'addan domin ɗaukar fansa kan kisan manyan sojoji
  • Mazauna garin Askira Uba sun yaba da yadda dakarun sojin suka ɗauki matakin gaggawa yayin da yan ISWAP suka shigo

Borno - Sojojin Najeriya sun sheke babban kasurgumin kwamandan mayakan ISWAP da wasu da dama a Asikira Uba, jihar Borno.

Daily Nigerian ta rahoto cewa sojojin sun kai hari kan yan ta'addan ba ƙaƙƙautawa domin ɗaukar fansa, bayan kisan da suka yi wa manyan jami'an soji.

Mayakan ISWAP sun kashe birgediya Janar Dzarma Zirkushi, da kwamandan 28 Task Force da wasu manyan sojoji uku ranar Asabar yayin da suke kan hanyar kaiwa sojiji ɗauki a kauyen Bungulwa, kusa da Askira Uba.

Kara karanta wannan

Borno: Yadda samamen sojoji a sansanin ISWAP ya janyo halakar sojoji

Sojojin Najeriya
Harin Fansa: Sojojin Najeriya sun hallaka kasurgumin kwamandan yan ta'adda da wasu 37 a Askira Hoto: punchng.com
Asali: UGC

PRNigeria ta rahoto cewa dakarun sojin sun shirya, cikin dabaru da ƙara karfi suka mamayi kwamandan ISWAP, kuma suka kashe baki ɗaya mayakansa a Askira Uba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan ta'adda nawa sojojin suka kashe a harin?

Wata majiya daga jami'an sojojin ya tabbatar da cewa aƙalla gawarwakin yan ta'adda 30 aka tattara, yayin da dakarun sojin suka cigaba da mamaye dazukan dake Askira.

Jami'in ya kara da cewa motocin yaki kusan 9, da makamin MRAP da wasu manyan makamai sojijin suka ragargaza ko kuma suka kwato a harin.

Yace:

"Da safiyar yau, lokacin da muke tsaftace yankin, mun kidaya gawarwaki 37 na yan ta'addan, yayin da wani babban kwamandansu da aka kamo domin bincike ya mutu a tsare."
"Hakanan mun kwato gomman manyan makamai daga hannun yan ta'addan yayin harin."

Ya mutane ke ciki a Askira?

Kara karanta wannan

Wasu 'yan ta'adda sun rantse ba za mu samu zaman lafiya ba, Cike da kunar rai Zulum ya magantu

Rahotanni sun tabbatar da cewa komai ya koma dai-dai a Askira, domin mazauna ƙauyen su yaba da ɗaukar matakin gaggawa cikin gwarzantaka da sojoji suka yi.

A cewar mazauna kauyen komai ya koma kamar da bayan mummunan harin da yan ta'addan suka kai, kuma sojoji suka tarbe su.

A wani labarin kuma Mutum 6 sun mutu yayin da wasu tsagerun yan bindiga suka sake kai sabon hari jihar Katsina

Mazauna yankin sun tabbatar da cewa maharn sun shiga ƙauyen Gwarjo, ƙaramar hukumar Matazu da daddare.

Har zuwa yanzun rundunar yan sandan jihar ba ta ce komai ba game da harin, yayin ƙauyuka ke cigaba da fuskantar matsaloli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel