Wasu 'yan ta'adda sun rantse ba za mu samu zaman lafiya ba, Cike da kunar rai Zulum ya magantu

Wasu 'yan ta'adda sun rantse ba za mu samu zaman lafiya ba, Cike da kunar rai Zulum ya magantu

  • Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno ya jajanta wa sojoji a kan mutuwar wasu daga cikin jami’ansu, manya da kanana a jihar
  • Mayakan ISWAP a ranar Asabar suka halaka Bigediya janar Dzarma Zirkusu wanda kwamandan runduna ta 28 ne da kuma wasu sojoji 3
  • A takardar wacce kakakin gwamnan, Isa Gusau ya fitar, ya ce gwamna Babagana ya nuna godiyarsa a kan sadaukarwar da sojojin su ka yi a jihar

Borno - Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya jajanta wa sojoji akan mutuwar wasu manya da kananun soji a jihar.

Mayakan ISWAP sun halaka Dzarma Zirkusu, wani bigediya janar kuma kwamandan runduna ta 28 na Task Force da wasu sojoji 3 daban a ranar Asabar.

TheCable ta ruwaito cewa, mayakan ISWAP din sun afka wa garin Askira da ke karamar hukumar Askira Uba.

Read also

Kano ta yi cikar kwari yayin da mataimakin gwamna ya aurar da ‘yarsa

Wasu 'yan ta'adda sun rantse ba za mu samu zaman lafiya ba, Cike da kunar rai Zulum ya magantu
Wasu 'yan ta'adda sun rantse ba za mu samu zaman lafiya ba, Cike da kunar rai Zulum ya magantu. Hoto daga thecable.ng
Source: UGC

An samu rahoto akan yadda kwamandan yake hanyar zuwa karfafa wa rundunar ya fada tarkon miyagun, TheCable ta wallafa.

A takardar wacce kakakin gwamnan, Isa Gusau ya bayyana, ya ce Babagana ya nuna godiyarsa a kan sadaukarwar da rundunar ta yi wa jihar Borno.

A cewarsa gwamnatin za ta ci gaba da tallafawa don samar don akwai bukatar sojoji sun nunka kokarinsu a jihar.

“Mummunan lamarin da ya faru yau a karamar hukumar Askira-Uba ya tuna mana yadda sojojinmu, jami’an tsaro, ‘yan sa kai da sauran mutanen da suke bayarwa don kawo zaman lafiya a wasu bangarorin jihar, akwai wasu ‘yan ta’adda da suke kokarin ganin sun kara hargitsa jihar,” a cewarsa.
“Burin wadannan ‘yan ta’addan shine su addabe mu ta yadda za mu mayar da hankulanmu akan su amma sakamakon addu’o’i da kuma bayanai daga mutanen jihar Borno abubuwa sun fara daidaita. Don haka ya kamata jami’an tsaro su kara dagewa.

Read also

Na jinjinawa bajintarsu: Buhari ya yi makokin sojojin da mayakan ISWAP suka kashe

“Muna godiya ga jami’an tsaronmu sannan muna ta’aziyya ga iyalan jami’an tsaro wadanda muka rasa a yau.”

Hukumar Sojin Najeriya ta tabbatar da kisan Birgediya Janar a harin kwantan baunar ISWAP

A wani labari na daban, hukumar Sojin Najeriya tabbatar da kisan Birgediya Janar Dzarma Zirkushu, Kwamandan rundunar 28 Task Force Brigade, dake Chibok, jihar Borno, Arewa maso gabas.

Yan ta'addan sun kashe Janar din tare da wasu jami'ansa uku, yayinda suke hanyar =su ta zzuwa kai dauk ga Sojoji a kauye Bungulwa dake kusa Askira Uba.

Kakakin hukumar Sojin Najeriya, Onyeama Nwachukwu, ya sanar da hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar, rahoton DailyNigerian.

Source: Legit.ng

Online view pixel