Borno: Yadda samamen sojoji a sansanin ISWAP ya janyo halakar sojoji

Borno: Yadda samamen sojoji a sansanin ISWAP ya janyo halakar sojoji

  • Luguden wutan da rundunar sojin Najeriya ta yi wa mayakan ISWAP shi ya janyo mayar da martani da yayi ajalin janar 1 da wasu sojoji 3
  • 'Yan ta'addan sun yi kwanton bauna a hanyar garin Askira Uba inda suka kai wa tawagar Janar Zirkusu farmaki, suka halaka shi da wasu soji 3
  • An tattaro cewa, luguden wuta sojin sama suka yi wa 'yan ta'addan yayin da suke tsaka da taro da Sani Shuwaram, sabon shugabansu a tafkin Chadi

Borno - Samamen da rundunar sojin Najeriya ta kai wa mayakan ISWAP har sansanin 'yan ta'addan ya janyo kisan Birgediya Janar Dzarma Zirkusu da wasu sojoji uku, majiyoyi masu karfi suka sanar da Daily Trust.

Mai magana da yawun rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace sojojin sun halaka 'yan ta'addan ISWAP yayin arangamar.

Kara karanta wannan

Wasu 'yan ta'adda sun rantse ba za mu samu zaman lafiya ba, Cike da kunar rai Zulum ya magantu

Borno: Yadda samamen sojoji a sansanin ISWAP ya janyo halakar sojoji
Borno: Yadda samamen sojoji a sansanin ISWAP ya janyo halakar sojoji. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ya ce baya ga kashe 'yan ta'addan, dakarun sojin sun tarwatsa motocin yakinsu.

Amma kuma, mayakan ta'addancin a ranar Asabar wurin karfe 9 na safe sun kai farmakin kwanton bauna kan tawagar Birgediya Janar Zirkusu yayin da suke hanyar zuwa garin Askira Uba domin samar da taimako ga dakarun da ake kai wa hari.

Majiyoyi sun sanar da Daily Trust cewa, hare-hare daban-daban na ranar Asabar din da 'yan ta'addan suka kai duk na daukar fansa ne.

"Sun matukar fusata a kan abinda ya faru da su a ranar Juma'a.
"An halaka kwamandojin ISWAP masu tarin yawa kuma wasu daga cikinsu sun raunata a ranar Juma'a ta hanyar luguden da aka yi musu yayin da suke tsaka da taro da sabon shugabansu Sani Shuwaram.

Kara karanta wannan

Na jinjinawa bajintarsu: Buhari ya yi makokin sojojin da mayakan ISWAP suka kashe

"Suna taro ne a wani wuri a arewacin Borno yayin da aka kai musu samame ta sama a Sabon Tumbun da Jibularam a karamar hukumar Marte ta jihar Borno," majiyar tace.

An tattaro cewa, mayakan ISWAP sun mamaye wani yanki na tafkin Chadi tun bayan da aka kashe shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau yayin wani fadan cikin gida tsakanin kungiyoyin biyu a farkon wannan shekarar.

Luguden wutar jiragen NAF ya yi sanadin mutuwar shanu 1500 a Taraba

A wani labari na daban, kusan shanu 1500 ne aka rasa sakamakon luguden ruwan wutar da sojojin sama suka yi a wata rugar Fulani da ke karamar hukumar Takum ta jihar Taraba.

Daily trust ta tattaro cewa, jiragen yakin sun kaddamar da luguden wutan kan gidajen Fulani makiyaya da ke wurin Kashinbila da Tor Donga a ranakun Laraba da Alhamis inda suka kashe shanu 1500.

An gano cewa, sun saki ruwan wutan ne wurin karfe 11 na safe da kuma hudu na yammacin Laraba da Alhamis.

Kara karanta wannan

Hotuna da sunayen jaruman Sojojin da aka kashe a artabu da yan ta'adan ISWAP

Asali: Legit.ng

Online view pixel