Yan sanda sun bindige wani mai garkuwa da mutane da yayi kokarin tserewa a jihar Niger

Yan sanda sun bindige wani mai garkuwa da mutane da yayi kokarin tserewa a jihar Niger

  • Jami'an yan sanda sun yi nasarar bindige wani mai garkuwa da mutane da yayi kokarin tserewa tare da kama wasu hudu a karamar hukumar Bosso da ke jihar Niger
  • Kwamishinan yan sandan jihar, Mista Monday Kuryas wanda ya tabbatar da lamarin a garin Minna, ya ce maharan sun yi garkuwa da wasu mutane biyu a ranar Alhamis
  • Ya ce tuni aka tura jami'an da ke yaki da masu garkuwa da mutane domin ceto mutanen da abun ya ritsa da su

Jihar Neja - Yan sanda a jihar Niger sun bindige wani da ake zaton mai garkuwa da mutane ne wanda ya nemi tserewa a karamar hukumar Bosso da ke jihar.

Lamarin wanda ya afku a ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba, ya kai ga kamun wasu mutane hudu, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Da dumi-daumi: 'Yan bindiga sun kai hari gefen FUT Minna, sun tafka mummunan barna

Yan sanda sun bindige wani mai garkuwa da mutane da yayi kokarin tserewa a jihar Neja
Yan sanda sun bindige wani mai garkuwa da mutane da yayi kokarin tserewa a jihar Neja Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Kwamishinan yan sandan jihar, Mista Monday Kuryas, ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya a garin Minna, babbar birnin jihar cewa wadanda ake zargin sun yi garkuwa da mutane biyu a ranar Alhamis.

Jami'ar fasaha ta tarayya da ke jihar na da matsuguni ne a karamar hukumar ta Bosso.

Kuryas ya kuma bayyana cewa an tura tawagar yan sanda da ke yaki da sace-sacen mutane da yan banga domin su ceto mutanen da aka sace, a ruwayar Theeagleonline.

Ya ce:

"Tuni muka tura tawagar da ke yaki da masu garkuwa da mutane domin ganin an ceto wadanda aka sace da kuma kama masu garkuwa da mutanen da suka tsere.
"Abun bakin ciki, an harbi wani mai wucewa yayin musayar wuta tsakanin yan sanda da masu garkuwa da mutanen.

Kara karanta wannan

Basaraken Katsina da wani dalibi sun samu yanci bayan kwanaki 26 a hannun masu garkuwa da mutane

"Muna rokon samun karin goyon baya da hadin kai daga jama'a, musamman mazauna kakkara. Su bamu sahihan bayanai da zai taimaka wajen kama miyagu a tsakaninsu.
"Mun shirya yaki don tunkarar duk wani mutum ko kungiyar yan ta'adda da ke tayar da zaune tsaye a jihar."

'Yan bindiga sun kai hari gefen FUT Minna, sun tafka mummunan barna

A baya mun kawo cewa wasu tsagerun 'yan bindiga sun kai wani hari yankin Gidan-Kwano, gefen jami'ar fasaha ta tarayya (FUT) da ke garin Minna, babbar birnin jihar Neja.

Maharan sun halaka mutum daya sannan sun yi garkuwa da wasu mutane biyu a harin, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kai tsaye maharan suka kaddamar da ta'asarsu a gefen babban mashigin jami'ar kuma an tattaro cewa daliban da ke zama a wajen makarantar sun fi yawa ne a garin da lamarin ya afku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel