Da dumi-dumi - Direba ne ya banke dan jaridar Vanguard da ya bata, inji 'yan sanda

Da dumi-dumi - Direba ne ya banke dan jaridar Vanguard da ya bata, inji 'yan sanda

  • Hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa wani direban mota ne halaka dan jaridar Vanguard, Tordue Henry Salem
  • A ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba, ne aka tsinci gawar Salem a babban asibitin wuse
  • Yayin da aka gurfanar da shi, direban ya bayyana cewa ya banke dan jaridar ne a yankin Mabushi a ranar 13 ga watan Oktoba sannan ya tsere

Abuja - Hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewa wani direban mota ne ya kashe dan jaridar Vanguard, Tordue Henry Salem, wanda aka tsinci gawarsa a ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba, The Nation ta rahoto.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan kasar, CP Frank Mba, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 12 ga watan Nuwamba, yayin da yake gurfanar da direban a harabar rundunar IRT da ke Guzape, Abuja.

Kara karanta wannan

Za a kai shugaban cibiyar da ya yi shekara 18 yana cin albashi da takardun bogi kotu

Da dumi-dumi - Direba ne ya banke dan jaridar Vanguard da ya bata, inji 'yan sanda
Da dumi-dumi - Direba ne ya banke dan jaridar Vanguard da ya bata, inji 'yan sanda Hoto: Vanguard NGR
Asali: Facebook

Mba ya bayyana cewa an gano gawar Salem ne a babban asibitin Wuse.

A ruwayar Punch, ta ce a yayin gurfanar da shi, direban mai suna Itoro ya bayyana cewa ya banke dan jaridar ne a yankin Mabushi a ranar 13 ga watan Oktoba, sannan sai ya tsere.

An gano gawar ɗan jaridar Nigeria, Salem, da ya ɓace

A baya mun kawo cewa, an gano gawar dan jaridar Vanguard da ke dakko rahotanni daga Majalisar Tarayya, kimanin wata daya dabacewarsa.

An yi wa Tordue Salem ganin karshe da ransa ne a kusa da gidan man Total da ke kusa da hedkwatar rundunar yan sanda ta Abuja a ranar 13 ga watan Oktoban 2021.

An kama wasu mutane ciki har da wani Prince Enyenihi da ake zargi da hannu a bacewarsa.

Kara karanta wannan

An shigar da Hafsat Barauniya kotu kan amsar kudi amma taki yin aikin

Asali: Legit.ng

Online view pixel