Za a kai shugaban cibiyar da ya yi shekara 18 yana cin albashi da takardun bogi kotu

Za a kai shugaban cibiyar da ya yi shekara 18 yana cin albashi da takardun bogi kotu

  • A yau Juma’a ake sa ran cewa Lauyoyin ICPC za su gurfanar da Chima Igwe a wani kotu da ke Legas.
  • Ana tuhumar Chima Igwe da amfani da satifiket din PhD ne karya wajen samun karin matsayi a aiki.
  • Bincike ya nuna da wannan takarda na bogi ne jami’in ya rika amfani, har aka nada shi DG a FIIRO.

Abuja - Watakila hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashin gaskiya a Najeriya ta gurfanar da tsohon shugaban cibiyar FIIRO, Chima Igwe a gaban kotu.

A ranar Juma’a, 12 ga watan Nuwamba, 2021, jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa akwai yiwuwar ayi shari’a da Chima Igwe a dalilin amfani da takardar bogi.

Chima Igwe ya yi amfani da takardun digirin PhD na karya, ya yaudari hukuma, ya yi shekara dai-daya har 18 yana ta karbar albashi ba tare da an gane ba.

Kara karanta wannan

Gumi ya caccaki 'yan aware: Igboho da Kanu ne suka kunna wutar rikicin Fulani a kudu

Rahoton na PUNCH Metro yace za a gurfanar da Igwe ne a gaban Alkali mai shari’a, Sherifat Solebo ta babbar kotun jihar Legas da ke zama a garin Ikeja.

Hukumar ta ICPC za ta kafa hujja ne da amfani da takardun PhD na bogi wajen samun mukmami. Wannan aikin rashin gaskiya ne wanda ya saba dokokin kasa.

FIIRO
Cibiyar FIIRO da aka kafa a 1956 Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ta ina aka bankado asirin Chima Igwe?

Head Topics tace Igwe ya fara samun matsala ne bayan tsohuwar shugabar makarantar FIIRO da ke Oshohi, Farfesa Gloria Elemo ta sauka daga kujerar ta a 2019.

A lokacin ne Minista ya nada shi a matsayin shugaban rikon kwarya na FIIRO. Wannan ya jawo aka fara bincike a kan digirin na PhD da yake takama da shi.

Majalisar da ta ke sa ido a kan aikin cibiyar ta hana a tabbatar da Igwe a matsayin darekta. Daga nan ICPC ta shiga binciken yadda aka yi shekara 18 yana aiki.

Kara karanta wannan

Majalisa ta kawo dabarar hana magudin zabe, za a rika aiki da na’ura wajen tattara kuri’u

Binciken da hukumar ICPC tayi

Binciken da jami’an hukumar ICPC suka yi ya tabbatar da cewa ikirarin Igwe na cewa ya samu PhD ne daga jami’ar D’Abomey Calavi, sam ba gaskiya ba ne.

A lokacin da ya kawo wannan satifiket na bogi, ba a bude wannan jami’a ta kasar Benin a Duniya ba. Kawo yanzu dai ICPC ba tace komai ba a kan batun shari’ar.

Lucky Nosakhare Igbinedion ya koma gidan jiya

A jiya da yamma aka ji cewa hukumar EFCC ta sake taso keyar tsohon Gwamnan Edo, Lucky Nosakhare Igbinedio, wanda ya taba shiga kurkuku, ya fito.

Wannan karo ma an tsare Cif Lucky Igbinedion a hedikwatar hukumar EFCC ne domin ya amsa wasu tambayoyi game da zargin ya saci wasu kudi a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel