Yadda 'yan bindiga suka fasa gilashin mota suka yi awon gaba da hamshakiyar 'yar kasuwa

Yadda 'yan bindiga suka fasa gilashin mota suka yi awon gaba da hamshakiyar 'yar kasuwa

  • ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wata ‘yar kasuwa, Christiana Bernard a wuraren babban gidan talabijin din jihar Ribas na NTA da ke Port Harcourt, babban birnin jihar
  • Rahotanni sun nuna yadda ‘yan bindigan su ka kai wa Bernard farmaki ta na tsaka da tuki a harabar gidan ta a ranar Laraba inda su ka ragargaje gilashin tagar motar
  • Sun yi hakan ne bayan sun bukaci ta bude kofar motar amma ta murje ido ta ki, daga nan su ka tsere da ita tare da motar kirar Honda Crosstour, wacce daga baya aka tsinta

Jihar Ribas - ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wata ‘yar kasuwa, Christiana Bernard a wuraren babban gidan talabijin din jihar Ribas na NTA da ke Port Harcourt.

Kara karanta wannan

Borno: Dan majalisa a ya bayyana yadda 'yan ISWAP suka kone gidan da ya ginawa dan uwansa

The Punch ta tattaro bayanai akan yadda su ka kai farmakin yayin da Bernard ta ke tuka motar ta a harabar gidan su a ranar Laraba.

'Yan bindiga sun fasa gilashin mota sun yi awon gaba da hamshakiyar 'yar kasuwa
'Yan bindiga sun fasa gilashin mota sun yi awon gaba da hamshakiyar 'yar kasuwa a Rivers. Hoto: The Punch

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyoyi sun bayyana yadda ‘yan bindigan su ka kai mata farmaki inda su ka bukaci ta bude kofar motarta amma ta yi kunnen uwar-shegu da su.

Cikin hassala su ka ragargaje gilashin tagar motar sannan suka tsere da ita cikin motar kirar Honda Crosstour.

Har yanzu ba su kira don fadin kudin fansa ba

A cewar daya daga cikin majiyoyin:

“Na kira daya daga cikin abokai na da ke kusa da gidanta inda ya ce ‘yan bindiga sun kai mata farmaki ne tana hanyar komawa gida daga shagonta.
“Har jami’in tsaro su ka nuna wa bindiga tare da umartar sa da ya kwanta kasa. Sun fasa tagar motar ta daga nan su ka shige motar tare da tserewa da ita.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

“Daga baya an tsinci motar wuraren titin Air Force da ke Port Harcourt. Har yanzu dai babu wanda su ka kira don fadin kudin fansa. Muna fatan dawowarta lafiya.”

Jami’ar hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, Nnamdi Omoni ta yi alkawarin bincike akan lamarin sannan ta sanar da wakilin Punch.

Har lokacin rubuta rahoto ba a ji komai ba daga wurinta.

'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe

A wani labarin, 'yan sanda sun yi ram da samari 2 bisa kama su dumu-dumu da laifin sare wa juna hannaye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

An ruwaito yadda ‘yan sandan su ka kama Adamu Mohammed da Bukar Audu, bayan sun datse wa juna hannaye yayin wani fada da su ka tafka a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An bindige mutane biyar yayin da jihar Imo ta sake daukar zafi

Premium Times ta bayyana yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, a ranar Litinin a Damaturu ya bayyana a wata takarda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel