Mahaifiyar Hameed Ali, shugaban kwastam ta riga mu gidan gaskiya

Mahaifiyar Hameed Ali, shugaban kwastam ta riga mu gidan gaskiya

  • Labarin da muke samu ya ce, kwanturola janar na hukumar kwastam ya yi rashi, Allah ya yiwa mahaifiyarsa rasuwa
  • A cikin wani bidiyon da aka yada, an lokacin da ake jana'izarta a masallacin An-Noor da ke Maitama a Abuja
  • Hakazalika, jana'izar ta samu halartar 'yan uwa da abokan arziki, ciki har da jami'an gwamnati da dama

Abuja - Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, Hameed Ali, kwanturola janar na hukumar tsaron iyaka ta kwastam ya rasa mahaifiyarsa Hajiya Aisha Ali.

A cikin wani bidiyo da hukumar kwastam ta yada a shafinta na Facebook, Legit.ng Hausa ta gano lokacin da ake jana'izar mahaifiyar ta Hameed Ali, inda rahoton ya ce an yi jana'izar ne a masallacin An-Noor da ke Wuse a Abuja.

Mahaifiyar Hameed Ali, shugaban kwatsam ta riga mu gidan gaskiya
Shugaban hukumar INEC, Hmeed Ali | Hoto: aminiya.dailytrust.com
Source: UGC

Hakazalika, jana'izar ta samu halartar manyan iyalai, 'yan uwa da abokan arziki kana da jiga-jigan gwamnati.

Read also

Yan bindiga sun yi awon gaba da ma'aikatan gwamnatin Kaduna a Zaria, dukkansu mata

Anga jama'a da yawa na mika ta'aziyya da makoki bayan sallar jana'aizar.

Idan ba a manta ba, a shekarar 2018 ne Hameed Ali ya yi rashin matarsa mai suna Hajiya Jummai Ali.

Hajiya Jummai ta rasu tana da shekaru 53, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Allah ya yiwa Dan Makwayon Kano, Alhaji Sarki Aminu Bayero, rasuwa

A wani labarin, Allah yayiwa Alh. Sarki Aminu Bayero mai saurautar Dan Makwayon Kano rasuwa da daren Talata, 27 ga watan Oktoba, 2021.

Legit ta tattaro daga Jikokinsa akalla biyu wanda suka tabbatar da rasuwar marigayin.

Aminu Ali Muhd a shafinsa na Facebook, ya bayyana mutuwar kakansa kuma ya bukaci al'umma su roka masa Aljannah.

Source: Legit.ng

Online view pixel