Allah ya yiwa Dan Makwayon Kano, Alhaji Sarki Aminu Bayero, rasuwa

Allah ya yiwa Dan Makwayon Kano, Alhaji Sarki Aminu Bayero, rasuwa

Jihar Kano - Allah yayiwa Alh. Sarki Aminu Bayero mai saurautar Dan Makwayon Kano rasuwa da daren Talata, 27 ga watan Oktoba, 2021.

Legit ta tattaro daga Jikokinsa akalla biyu wanda suka tabbatar da rasuwar marigayin.

Aminu Ali Muhd a shafinsa na Facebook, ya bayyana mutuwar kakansa kuma ya bukaci al'umma su roka masa Aljannah.

Yace:

"Kakana ya rasu yau, Dan Makwayon Kano Alh. Abdullahi sarki Aminu. Dan Allah kowa yayi masa addu'a. Allah ya yi masa matsaya mai girma a Aljannah."

Wani kuma Umar Ali Muhd yace:

"Kakanmu Dan Makwayon Kano Alh. Abdullahi sarki Aminu. Ku taimaka mana da addu'a."

Read also

Da dumi: Yan Boko Haram sun yi dira garin Katarko a jihar Yobe yau Asabar

An ruwaito cewa za ayi jana'izar sa karfe 4:00 a Kofar Kudu.

Allah ya yiwa Dan Makwayon Kano, Alhaji Sarki Aminu Bayero, rasuwa
Allah ya yiwa Dan Makwayon Kano, Alhaji Sarki Aminu Bayero, rasuwa Hoto: Umar Ali Muhd
Source: Facebook

Source: Legit

Online view pixel