Yan bindiga sun yi awon gaba da ma'aikatan gwamnatin Kaduna a Zaria, dukkansu mata

Yan bindiga sun yi awon gaba da ma'aikatan gwamnatin Kaduna a Zaria, dukkansu mata

  • Duk da katse layukan waya da rufe kasuwanni a jihar Kaduna, yan bindiga na cigaba da cin karensu ba babbaka
  • A ranar Litinin wasu yan bindiga sun tare motar ma'aikatan gwamna a hanyar Zaria kuma sun kwashesu gaba daya
  • Iyalan wadanda aka sace sun ce direban kadai aka saki don ya isar da labari ga gwamnati

Zaria, jihar Kaduna - Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da iyaye mata ma'aikatan gwamnatin jihar Kaduna yayinda suke hanyar tafiya cikin mota.

Daily Nigerian ta bayyana cewa wannan abu ya auku ne da yammacin Litinin misalin karfe 5 tsakanin Giwa da Zaria.

Rahoton ya kara cewa direba kadai yan bindiga suka saki ya tafi domin ya sanar da gwamnatin jihar da iyalansu abinda ya faru.

Legit ta tabbatar da wannan abu daga bakin wasu iyalan ma'aikatan da aka sace.

Kara karanta wannan

Abuja: Maciji ya sari ɗan babban limami a daji bayan ya tsere daga hannun masu garkuwa

Yan bindiga sun sace ma'aikatan gwamnatin Kaduna a Zaria
Yan bindiga sun yi awon gaba da ma'aikatan gwamnatin Kaduna a Zaria, dukkansu mata Hoto
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yusuf Aliyu yace:

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Matar mahaifina na cikin ma'aikatan gwamnatin karamar hukumar Zaria da aka sace. Ya Allah ka bayyana mana su cikin koshin lafiya."

Arewa Queen tace:

"An yi garkuwa da daya daga cikin yayyena yau a hanyar Giwa-zaria. Muna rokon Allah madaukakin sarki ya fitar da su cikin aminci da koshin lafiya."

Abdulhaleem Isa Ringim ya bayyana cewa:

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah Ubangiji ya kubutar masa da su Hajiya. Allah ya kubutar da su cikin aminci."

An kama sojan da ke da hannu a harin da aka kai har cikin NDA

A wani labarin kuwa, an ruwaito cewa, rundunar sojin sama ta kama Torsabo Solomon, wani Sajan da ake zargi da hannu a kai hari a makarantar horas da sojoji ta Najeriya (NDA) da ke Kaduna.

Kara karanta wannan

An kai sabon hari a Kaduna, an kashe mutane an ƙone gidaje da dama

An kashe jami’ai biyu, an kuma yi garkuwa da wani jami’i guda a lokacin da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai wa NDA hari a watan Agusta.

Wannan lamarin ya haifar da hargitsi a kasar tare da nuna damuwa game da karuwar rashin tsaro.

Majiyar soja ta shaida wa TheCable cewa an kama Solomon ne a ranar Litinin a NAF’s 153 BSG a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel