Ginin da ya kife a Legas: Rikici ya barke tsakanin Matar mamallakin ginin mai hawa 21 da yan uwansa kan kuɗi

Ginin da ya kife a Legas: Rikici ya barke tsakanin Matar mamallakin ginin mai hawa 21 da yan uwansa kan kuɗi

  • Mutane sun fara zuwa wuraren da ake kai gawar waɗan da suka mutu a ginin Legas, domin diba gawar yan uwansu
  • Matar mamallakin ginin da kuma wasu yan uwansa sun fara rikici kan gadon kuɗaɗensa da kuma motocinsa
  • Matar Mista Osibona dai ta dawo ne daga ƙasar Amurka bayan jin labarin mutuwar mai gidanta, daga nan rikicin ya soma

Lagos - A ranar Asabar, iyalan waɗan da dogon gini mai hawa 21 ya rufta da su, suka fara zuwa wuraren da aka ajiye gawarwaki domin duba na yan uwansu.

A wani bamgaren kuma matar Femi Osibona, wanda ke jagorantar ginin da yan uwansa suka fara rikici kan amfani da makuɗan kudin da ya bari, da kuma motocin alfarma dake cikin gidansa.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Mamallakin dogon gini mai hawa 21 da ya rushe a Legas ya mutu

Punch tace rikicin ya soma ne a gidan sa dake kan hanyar Mosley, Ikoyi, awanni 24 kacal bayan jami'an ceto sun gano gawarsa a baraguzan ginin.

Ginin da ya kife a Legas
Ginin da ya kife a Legas: Rikici ya barke tsakanin Matar mamallakin ginin mai hawa 21 da yan uwansa kan kuɗi Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ɗaya daga cikin wakilan mu, wanda ya ziyarci ɗakin aje gawarwakin da yammacin Asabar, yace tausayi da hawaye sun mamaye wurin yayin da iyalai da dama suka fara zuwa duba yan uwansu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga cikin waɗan da aka tabbatar da mutuwarsu akwai wata yar Bautar ƙasa, Zaynab Sanni Oyindamola, wani mai aikin saka ƙarfe, injiniya da kuma Faston cocin RCCG, Ola Ogunfunwa, da sauransu.

Mutun 9 aka ceto da ransu, inda aka sallami mutun uku bayan yi musu magani yayin da sauran shida ke kwance a asibitin Lagos Island.

An sake gano mutum 6 da ransu

Rahotanni sun bayyana cewa mutum shida aka ceto daga bayan nan an gaggauta kai su asibiti domin wasu daga cikinsu na gab da rasa rayuwarsu a ƙarƙashin baraguzan ginin.

Kara karanta wannan

Miyagun yan bindiga sun bi tsakar dare sun yi awon gaba da mata zalla a Neja

Mafi yawan waɗan da ake tsammanin yan uwansu na cikin waɗan da kifewar ginin ya rutsa da su, sun ziyarci babban asibitin Lagos Mainland.

Iyalan sun je wurin aje gawarwaki na asibitin domin diba ko akwai yan uwansu cikin waɗan da jami'an ceto suka gano zuwa yanzun.

Yadda asibitin ya taimaka wa iyalan

Ɗaya daga cikin ma'aikatan asibitin, wacce aka ɗora wa alhakin taimakawa iyalan ta rinka kirna su ɗaya bayan ɗaya domin duba gawarwakin.

Kafin fara aikinta, matar ta sanar musu da cewa:

"Zamu bukaci hoton wanda kuke nema da kuma kwafin ID Card ɗinsa, sai kuma mutum ɗaya daga cikin iyalansa na jini. Zamu kira ɗaya bayan ɗaya, amma sai kun jure."

Yadda rikici ya ɓarke a iyalan Osibona

Rikici ya ɓarke a cikin iyalan Osibona yayin da natarsa ta aure da kuma yan uwansa suka fara faɗa kan wanda zai gaji dukiyarsa.

Matar Osibona da ƴaƴansa sun isa gidansa tare da yan sanda kan dukiyar gado, wacce ta haɗa da motoci, makudan kuɗi, da sauran kadarori.

Kara karanta wannan

Shin dagaske kasurgumin dan bindigan da ya addabi Arewa, Dogo Gide, ya mutu? Gaskiyar abinda ya faru

Wata majiya dake kusa da iyalan, wanda ya tabbatar da rikicin ga wakilan mu, yace duk da maigidan ya yi irin wannan mutuwa, amma iyalansa sun koma rikici kan dukiyarsa.

Yace:

"Tabbas sun fara faɗa tsakanin su, matarsa tafi zama a waje. maimakon su maida hankali kan ginin da ya rushe, amma sun koma suna rikicin kan dukiyar da ya bari."

Wane hali ake ciki a wajen ginin?

Gwamnan Legas, Babajige Sanwo-Olu, yace zuwa ranar Asabar da yamma, an gano gawar mutum 42 daga cikin ɓaraguzan ginin.

Gwamnan yace an bibiyi asibitin da aka kai mutum 6 da aka sake ganowa a raye kuma an ɗauki bayanan su.

A sanarwan da kakakinsa ya fitar, gwamnan yace:

"An kai su asibitin yan sanda ne dake Falomo, kuma har an sallami wasu. Mun samu cikakken bayanansu, hakan yasa jumullan waɗan da suka tsira yakai 15."

Hakanan kuma ya bayyana cewa iyalai 49 suka cike fom ɗin rasa yan uwansu ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wani gini mai hawa-hawa ya sake ruftawa a jihar Legas

Wane mataki gwamnati zata ɗauka?

Ya kuma ƙara da cewa waɗan da iyalan suka kasa gane yan uwansu, tuni aka ɗauki gwajin kwayar halitta DNA domin tabbatarwa.

"Akwai kuɗin da gwamnati ta ware domin aikin jana'izar mutanen da suka mutu. Duk iyalan dake bukata za'a tallafa musu da shirye-shiryen jana'izan."
"Hakanan kuma waɗan da suka tsira da rayuwarsu gwamnati ta tallafa musu da kuɗaɗe domin fuskantar ƙalubalen rayuwa bayan tsira daga lamarin."

Bola Tinubu da gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, sun ziyarci wurin da lamarin ya faru bisa jagorancin gwamnan Legas.

A wani labarin kuma wata gobara da ta tashi a ɗakin kwanan ɗalibai mata na UMIMAID, ta jikkata mutum uku

Rahoto ya nuna cewa gobarar da ta ɓarke daga abin girki mai amfani da kalanzir, ta jikkata ɗalibai mata uku, kuma suna asibiti.

A cewar hukumar UNIMAID, tuni ta ɗauki matakai sosai domin kare lafiyar ɗalibanta daga irin haka a ɗakin kwanan su.

Kara karanta wannan

Gwamna El-Rufa'i ya rantsar da sabbin Ciyamomi 21 da suka lashe zaɓe a fadin jihar Kaduna

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel