Soyayya: Ƙwararan dalilai 4 da suke saka mata son miskilin namiji

Soyayya: Ƙwararan dalilai 4 da suke saka mata son miskilin namiji

  • Mutane da dama su kan kalli miskilin namiji a matsayin mutum mai aji, jin kai, raina mutane da wulakanci, yayin da ba lallai hakan ba ne, kawai halayya ce ta dan Adam
  • Duk da yadda jama’a ke sukar miskilai, mata da dama sun fi karkatar da tunanin su ta hanyar yin rububin su don wannan dabi’ar ta su ta na da mutukar daukar hankali
  • Akwai wasu sirruka da dalilai masu tafiya da imanin mata wanda idan namiji ya kasance miskili za ka ga har fada mata su ke yi akan sa, kuma hakan na da nasaba da wasu dabi’u kebabbu na miskilai

Kasancewar mutum miskili wata dabi’a ce ta daban wacce Ubangiji ya ke halittarsa da shi, kuma ana samu a bangaren maza ko kuma mata.

Bisa ruwayar mujallar Tozali, mata da dama suna karkatar da hankalinsu akan miskilin namiji inda zaka ga suna ta rububi akansa.

Kara karanta wannan

Babban dalilin da yasa mutane ke shafe-shafe don sauya launin fatarsu

Soyayya: Ƙwararan dalilai 4 da suke saka mata rububin miskilin namiji
Soyayya: Ƙwararan dalilai 4 da suke saka mata rububin miskilin namiji. Hoto: Daily Trust/Bulama
Asali: Facebook

Mujallar Tozali ta kara da bayyana yadda ake kallon namiji miskili a mutum mai wulakanta jama’a, raini da jin kai saboda dabi’arsa ta shiru-shiru.

Duk da wannan kallon da jama’a suke yi wa miskilan mutane, mata su kan karkatar da tunanin su akan namiji miskili fiye da mai fara’a da yawan magana.

Dalilan da yasa mata ke son miskilin namiji

Ga dai wasu dalilan da yasa mata ke son na miji idan sun fahimci miskili ne:

1. Miskilin mutum baya da shiga harkokin mutane saboda yanayinsa na rashin son yin yawan maganganu.

Rashin shiga harkokin jama’a kuma ya na kara wa mutum kwarjini da kima a idon kowa, hakan ya ke sa miskilai kima da daraja a idon mata.

2. Dabi’ar shiru-shirun miskilai tana basu damar sauraron mutane don haka su kan lakanci dabi’un jama’a.

Kara karanta wannan

Iko sai Allah: Bidiyon matasan fasinjoji 2 suna ba hammata iska a cikin jirgin sama

Lakantar dabi’ar mutane ya kan hana sa-in-sa ta shiga tsakanin jama’a. Saboda bukatar kwanciyar hankali mata ke karkata ga miskilai.

3. Miskilai su na da rike sirrin jama’a kuma ba su da korafi ko kuma mita akan abu daya, wannan dabi’ar ta na daukar hankalin mata.

Rashin yawan magana ke sa miskilai boye sirruka, mata kuma su na son masu boye sirri. Har ila yau rashin mitar ta kan sa mata fadawa tarkon son miskilai maza.

4. Miskilanci yana saka mutum ya zama mai hakuri da juriya a kan lamurra.

Wannan dalilin ya sa mata da dama suke son maza masu wannan halayyar don juriya ta na rike dankon soyayya ko aure ma.

Zugar Ƙawaye Na Bi: Ku Taya Ni Roƙon Mijina Ya Mayar Da Ni, Tsohuwar Matar Babban Sarki a Najeriya

A wani labarin, jun ji cewa Olori Damilola, tsohuwar matar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi ta fito fili ta bai wa basaraken da gidan sarautar hakuri.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun harbe mutum 7 har lahira a kauyen Adamawa

A wata takarda wacce ta wallafa ta shafin ta na Instagram a ranar Lahadi, sarauniyar ta bai wa gabadaya ‘yan uwan Adeyemi hakuri da kuma majalisar jihar Oyo.

Damilola, wacce ita ce amaryar basaraken, ta zargi gidan sarautar da nuna halin ko-in-kula akan ta da dan ta daya tal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel