Babban dalilin da yasa mutane ke shafe-shafe don sauya launin fatarsu

Babban dalilin da yasa mutane ke shafe-shafe don sauya launin fatarsu

  • Akwai manyan dalilan da su ke sanya mutane su na sauya launin fatar su, daga bakake zuwa farare, kuma yawanci ya na da alaka da yanayin mutanen da ke zagaye da mutum
  • Abokai, ‘yan uwa har da jama’an gari su kan yi amfani da sunaye na zolaya ga mutum musamman idan launin fatar sa ta kasance mai duhu kwarai
  • A wannan labarin mun tattaro babban dalilin da ya sa wasu su kan yanke shawarar amfani da mayuka na kamfanoni daban-daban wurin yin bilicin

Hakika babu wanda ya ke daukar wani mataki a rayuwar sa ba tare da wani kakkwaran dalili ba. Don haka har masu sauya launin fatar su su na da manyan dalilan yin hakan.

An taba kiran ka da bilaki? Duna na lillahi? Dan baki ko kuma ‘yar baka? Saboda launin fatar ka ta na da duhu? Yayin da ake kiran wasu fararen da bature, Dan fari da sauran su.

Read also

Nasara daga Allah: An bindige mai garkuwa da mutane yayin karbar kudin fansa

Babban dalilin da yasa mutane ke shafe-shafe don sauya launin fatarsu
Babban dalilin da yasa mutane ke shafe-shafe don sauya launin fata. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Bisa ruwayar Daily Trust, ya kamata a matsayin mu na ‘yan Najeriya, mu rungumi bakaken fatocin mu kuma mu dena amfani da kalaman nan don su kan yi tasiri a zukatan wadanda ake furta ma wa.

Duk da illolin bilicin, Daily Trust ta bayyana yadda ya karade ko ina. Yanzu haka kamfanonin mayukan bilicin su na matukar ciniki.

Kalamai su kan yi tasiri a zukatan masu sauraro shiyasa wasu su ke kasa jurewa su dauki matakin yin bilicin.

Kuma kalaman su kan hana mutum kwanciyar hankali musamman yadda ake zaulayar bakaken fata, don haka wasu ke daukar mataki.

Maganganun jama’a su kan sa wasu su garzaya kasuwa don siyan mayuka, sabulai, allura wasu har kwayoyi don mallakar fata mai haske.

Read also

Rashin tsaro: Gwamnatin Zamfara ta hukunta mutane sama da 1, 000 da suka saba doka

Wannan dalilin ya sa kamfanonin da su ke hada mayuka na bilicin kullum su ke kara daukaka da bunkasa a kasashen bakaken fata.

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari.

A wani rahoton, wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta 5 duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Source: Legit.ng

Online view pixel