'Yan bindiga sun harbe mutum 7 har lahira a kauyen Adamawa

'Yan bindiga sun harbe mutum 7 har lahira a kauyen Adamawa

  • Rayuka 7 sun salwanta sakamakon farmakin da 'yan bindiga suka kai Bolki da ke karamar hukumar Numan a Adamawa
  • Miyagun dauke da bindigogi sun bude wa jama'a wuta a yankin Negga wurin karfe 11 na daren Talata inda suka raunata wasu
  • Majalisar jihar Adamawa ta yi Allah wadai da wannan farmakin yayin da kakakin 'yan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar harin

Numan, Adamawa - A kalla rayuka bakwai ne wasu miyagun 'yan bindiga suka harbe a gundumar Bolki ta karamar hukumar Numan a jihar Adamawa.

Miyagun dauke da makamai sun kai farmaki yankin Negga ne wurin karfe 11 na daren Talata kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

'Yan bindiga sun harbe mutum 7 har lahira a kauyen Adamawa
'Yan bindiga sun harbe mutum 7 har lahira a kauyen Adamawa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wata majiya ta sanar da Daily Trust cewa, farmakin da miyagun suka kwashe sama da sa'a daya suna kaiwa ya bar mutane masu tarin yawa da miyagun raunika.

Kara karanta wannan

Dakarun Hisbah sun damke karuwai 44, sun kwace kwalaben Barasa 684 a Jigawa

Majalisar jihar Adamawa ta yi Allah wadai da farmakin inda ta yi kira kan inganta tsaron yankin baki daya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mataimakin kakakin majalisar, kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar Numan, Pwamwakeno Mackondo, ya yi kira ga sojoji da su kafa sansani a yankunan da suka yi fama da farmakin daban-daban.

A yayin tabbatar da aukuwar harin, mai magana da yawun rundunar 'yan sanda jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje, ya ce wasu mutum bakwai sun samu raunika kuma suna samun kulawar masana kiwon lafiya a asibiti.

Ya ce an tura 'yan sanda yankin domin kwantar da tarzoma tare da dawo da zaman lafiya yayin da suka fara bincike.

Jami'an tsaro sun dira gidan alkalin kotun koli a Abuja

A wani labari na daban, jami'an tsaro a ranar Juma'a sun dira gidan Mary Odili, alkali a kotun koli da ke Abuja. Alkalin kotun kolin mata ce ga Peter Odili, tsohon gwamnan jihar Ribas wanda a halin yanzu ya ke cikin wadanda hukumar yaki da rashawa ta kasa, EFCC suka sanya wa ido.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun zagaye wurin Ibada, sun buɗe wa mutane wuta a jihar Kaduna

Kamar yadda TheCable ta wallafa, Har yanzu dai babu cikakken bayani kan abinda ke faruwa a gidan.

Kamar yadda wata majiya ta ce, jami'an tsaron da suka tsinkayi gidan sun hada da jami'an 'yan sanda da na sojojin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel