Iko sai Allah: Bidiyon matasan fasinjoji 2 suna ba hammata iska a cikin jirgin sama

Iko sai Allah: Bidiyon matasan fasinjoji 2 suna ba hammata iska a cikin jirgin sama

  • Wasu matasa majiya karfi guda biyu sun bai wa hammata iska yayin da suke cikin jirgin sama a sararin samaniya
  • Sun fara hayaniya ne kan wurin ajiye kayayyakin da ke cikin jirgin inda dukkansu suka fusata da juna, duk da ba a san tushen fada ba
  • Babu kakkautawa suka fara damben inda sauran fasinjojin suka taso tare da kokarin rabawa amma sun kasa rabuwa duk da kokarin da aka yi

Wani bidiyon maza biyu fasinjoji a cikin jirgin suna bai wa hammata iska a cikin jirgi ya karade kafafen sada zumunta.

Babu shakka mazan majiya karfi sun fusata da juna tunda bidiyo ya nuna yadda ake ta yin kokarin raba su amma abun ya ci tura.

Iko sai Allah: Bidiyon matasa 2 suna ba hammata iska a cikin jirgin sama
Iko sai Allah: Bidiyon matasa 2 suna ba hammata iska a cikin jirgin sama. Hoto daga shutterstock.com
Source: UGC

Kamar yadda aka gano, sun kwashi damben ne sakamakon hatsaniyar da suka samu tare da rashin jituwa wurin ajiye kayansu a cikin jirgin.

Read also

Tirkashi: Uwa ta kashe 'ya'yanta biyar saboda kishi, ta hadu da fushin alkali

A yayin da suka dinga naushin juna a wuraren kujerun zama na cikin jirgin, sauran fasinjoji sun taso inda suka dinga kokarin raba fadan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga bidiyon yadda lamarin ya kasance:

Kano: 'Yan sintiri sun yi ram da mutumin da ke bayyana wa mata al'aurarsa

A wani labari na daban, wata kungiyar 'yan sintiri a jihar Kano ta yi ram da wani mutum mai suna Sani Saleh wanda ake zarginsa da bayyana al'aurarsa a cikin jama'a.

Salisu Idris, mataimakin kwamandan 'yan sintirin da ke yankin Medile a karamar hukumar Kumbotso ta jihar ya sanar BBC cewa wanda ake zargin an dade ana nemansa bayan an samu korafi daga mata daban-daban kan aika-aikar da ya ke yi.

"A duk lokacin da ya ga kungiyar mata, kawai sai ya cire wandonsa. Kafin maza su bayyana a wurin, sai ya tsere," Idris yace.

Read also

'Yan sanda sun yi ram da mijin da ya soka wa matarsa almakashi, ta sheka lahira

"Daga bisani mun kama shi bayan ya hantari wasu gungun yara mata a ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamba," ya kara da cewa.

Source: Legit.ng

Online view pixel