Namiji da raino: Wani magidanci ya lakadawa diyarsa duka har Lahira saboda ya kasa lallashinta

Namiji da raino: Wani magidanci ya lakadawa diyarsa duka har Lahira saboda ya kasa lallashinta

  • Gwamnatin jihar Ogun ta damke wani mutumi da zargin ya hallaka ɗiyarsa ta cikinsa ta hanyar lakaɗa mata dukan kawo wuka
  • Gwamnatin ta kuma mika shi ga rundunar yan sanda domin cigaba da bincike, amma tuni ya amsa laifinsa
  • Matarsa ta bayyana cewa ta haɗa kai da mijinta wajen kashe yayansu biyu saboda talauci ya musu katutu

Ogun - Gwamnatin Ogun ta bayyana cewa ta damke wani magidanci, Sanjo, a yankin Osogbo, babban birnin jihar, bisa zarginsa da dukan yarsa har lahira.

Kwamishinan mata, yara da harkokin jin kai, Olubukola Olaboopo, a wata sanarwa da ta fitar, tace an cafke mutumin ɗan shekara 43 a yankin Alekuwodo.

A cewar sanarwan tuni ma'aikatar ta miƙa mutumin ga jami'an yan sanda domin gudanar da bincike, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Uwa ta kashe 'ya'yanta biyar saboda kishi, ta hadu da fushin alkali

Matsalar gidan Aure
Namiji da raino: Wani magidanci ya lakadawa diyarsa duka har Lahira saboda ya kasa lallashinta Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Olaboopo ta bayyana cewa ma'aikatarta ta samu labarin lamarin ta wata majiya, nan take jami'an gwamnati suka je suka kamo mutumin.

Ko me ya haɗa shi da yar tasa?

A cikin sanarwan, magidancin ya faɗi cewa ya auri matarsa ne a shekarar 2008 kuma Allah ya albarkace su da ƴaƴa 5.

Magidancin yace:

"Wannan shine karo na uku da na lakaɗa wa ɗaya daga cikin yayan mu duka ba da gangan ba kuma duk sun mutu."
"Matata ta bar mun yarinyar, sai ta kama kuka, na yi iya bakin kokarina wajen lallashin ta amma ta cigaba da kukan ta."
"Kawai sai zuciyata ta kufula ta raya mun wani abu, nan take na zane yarinyar yar kimanin watanni 2 kuma ta mutu, ni da matata muka binne ta a gona."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da mijin da ya soka wa matarsa almakashi, ta sheka lahira

Me matar mutumin tace?

Da aka binciki matar Sanjo, ta bayyana cewa 'ya'yan su hudu cikin biyar sun mutu, hakan yasa sauran guda ɗaya suke da shi.

Ta kuma ƙara da cewa ta amince wa mijinta su kashe biyu daga cikin yayansu saboda talauci ya musu yawa, yayin da suka yar da guda daya.

A wani labarin kuma A karo na biyu cikin wata ɗaya kacal, wata gobara ta tashi a ɗakin kwanan ɗalibai mata na jami'ar UNIMAID dake Maiduguri

Rahoto ya nuna cewa gobarar da ta ɓarke daga abin girki mai amfani da kalanzir, ta jikkata ɗalibai mata uku, kuma suna asibiti.

A cewar hukumar UNIMAID, tuni ta ɗauki matakai sosai domin kare lafiyar ɗalibanta daga irin haka a ɗakin kwanan su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel