Yadda wata wuta ta barke a dakin kwanan dalibai mata, ta jikkata mata da dama a UNIMAID

Yadda wata wuta ta barke a dakin kwanan dalibai mata, ta jikkata mata da dama a UNIMAID

  • A karo na biyu cikin wata ɗaya kacal, wata gobara ta tashi a ɗakin kwanan ɗalibai mata na jami'ar UNIMAID dake Maiduguri
  • Rahoto ya nuna cewa gobarar da ta ɓarke daga abin girki mai amfani da kalanzir, ta jikkata ɗalibai mata uku, kuma suna asibiti
  • A cewar hukumar UNIMAID, tuni ta ɗauki matakai sosai domin kare lafiyar ɗalibanta daga irin haka a ɗakin kwanan su

Maiduguri, Borno - Aƙalla dalibai mata uku ne suka jikkata yayin da wata wuta ta ɓarke a ɗakin kwanan su na Murtala female hostel ranar Asabar.

Tribune Online tace wannan shine matsar gobara ta biyu da aka samu a jami'ar Maiduguri (UNIMAID) cikin wata ɗaya tal.

Unimaid
Yadda wata wuta ta barke a dakin kwanan dalibai mata, ta jikkata mata da dama a UNIMAID Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Rahoto ya nuna cewa ana zargin wutar ta tashi ne daga rishon girki na kalanzir, amma cikin gaggawa jami'an kwana-kwana na jami'ar suka kashe ta.

Kara karanta wannan

Yadda wata yar bautar kasa NYSC, Zainab Sanni, ta mutu a Legas bayan ta guje wa matsalar tsaro a Borno

Wane mataki UNIMAID ta ɗauka?

Da yake magana game da faruwar lamarin, jami'in hulɗa da jama'a na jami'ar, Farfesa Danjuma Gambo, yace lamarin ya faru ne daga fashewar tukunyar aje kalanzir.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Farfesa Gambo ya bayyana cewa ɗalibai mata guda uku da lamarin ya shafa, yanzun haka suna ƙarƙashin kulawa da lafiya a asibiti, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Gambo, wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, ya ƙara da cewa hukumar jami'ar UNIMAID ta fara ɗaukar matakai domin kare faruwar haka nan gaba.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta rahoto Farfesa Gambo yace:

"Hukumar wannan jami'a ta ɗauki matakai wajen ƙara kayan kariya daga wuta a ɗakunan kwanan ɗaliban ta."

A wani labarin kuma yayin da muke cigab da kawo muku abinda ke wakana a Anambra, kun ji Yadda wasu fusatattun masu kada kuri'a suka garƙame ma'aikatan INEC a Anambra

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jami'an yan sanda sun kwace zauren majalisar dokoki, sun hana yan majalisu shiga

Rahoto ya bayyana cewa ma'aikatan ne suka nemi barin cibiyar tattara sakamakon gundumar Oko II domin su koma ofishin INEC.

Lamarin ya saitu ne bayan sojoji sun shiga lamarin, inda suka kwashe kayan aikin zabe masu muhimmanci zuwa ofis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel