Sama da gidajen man Kano 50 sun rufe yayin da karancin man fetur ke kara kamari

Sama da gidajen man Kano 50 sun rufe yayin da karancin man fetur ke kara kamari

  • Karancin man fetur ya dumfaro jihar Kano, yayin da matafiya suka fara makalewa a tashoshin mota a wasu sassan jihar
  • Direbobi sun shaidawa manema labarai cewa, gidajen man fetur sun rufe ne saboda fargabar karin farashin man fetur
  • A halin yanzu, rahoto ya ce akwai sama da gidajen mai 50 da aka rufe a wasu sassan jihar Kano cikin 'yan kwanakin nan

Kano - Mazauna babban birnin Kano da fasinjoji daga garuruwan da ke kusa kamar Wudil, sun makale saboda rashin samun ababen hawa sakamakon karancin man fetur a jihar.

Tsoron karin farashin man fetur da ake sayar da shi kan Naira 165 ya shafi masu ababen hawa da harkokin kasuwanci a jihar.

Daily Trust ta gano cewa sama da gidajen mai guda 50 ne aka rufe daga Wudil zuwa Kano kan babbar hanyar tarayya ta Maiduguri, inda aka ga gidajen man fetur shida ne kacal a bude.

Read also

Yanzu Yanzu: Masu zaben gwamnan Anambra sun yi biris, sun ki fitowa daga gidajensu don yin zabe

Sama da gidajen man Kano 50 sun rufe yayin da karancin man fetur ke kara kamari
Gidajen mai na shirin kara farashin famfo na man fetur | Hoto: dw.com
Source: UGC

Wasu masu ababen hawa sun shaida cewa fargabar tashin farashin man fetur ya sa ba za a iya samun motocin da fasinjoji za su hau ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani direban mota mai suna Abdullahi Idris da ke jigilar fasinjoji daga Wudil zuwa Kano, ya ce tun a ranar Asabar din da ta gabata, an samu karancin ababen hawa ga fasinjojin da ke tafiya daga Wudil zuwa birnin Kano.

A cewarsa:

“Ko a jiya (Asabar) mutane da yawa sun makale saboda babu abin hawa saboda karancin man fetur. Na ji ana shirin kara farashin famfon mai zuwa Naira 300.”

Wani direban mota da ke jigilar fasinjoji daga tashar mota ta Hotoro zuwa Wudil, Isah Mamman, ya ce batun karancin man fetur abu ne da aka kirkireshi da gangan.

A kalamansa:

“Kowace shekara za a samu karancin mai a tsakanin watan Nuwamba da Disamba. Me yasa haka? Domin gwamnati na son kara farashin famfo na mai ta yadda a karshen da mutane ke shan wahala ba za su yi korafi ba."

Read also

Harbi ya yawaita, matsanancin cunkoson titin a Onitsha bayan sojoji sun rufe dagar Niger

Sai dai a kwanakin baya, Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), Malam Mele Kyari, ya ce akwai sama da lita biliyan 1.7 na man fetur da kuma wasu lita biliyan 2.3 da ke zuwa, ya kuma yi watsi da rade-radin da ake yi na karancin man fetur.

Vanguard ta ruwaito cewa, NNPC ta kawar da fargabar cewa, za a samu karancin man fetur, amma ga yadda abubuwa ke sauyawa a mako na biyu a watan Nuwamba.

Farashin man fetur zai tashi kwanan nan, kungiyar yan kasuwan mai ta yi gargadi

A wani labarin, kungiyar 'yan kasuwar man fetur masu zaman kansu a Najeriya IPMAN, ta gargadi gwamnatin tarayya cewa da yiwuwan farashin man fetur ya tashi kwanan nan.

Kungiyar tace hakan zai faru ne saboda masu defot sun kara farashi daga wajensu. Shugaban IPMAN na reshen Kano, Alhaji Bashir Danmallam, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a, rahoton Punch.

Read also

Rushewar benen Ikoyi: Yawan mamata ya kai 20, ana kokarin ceto wasu a cikin ginin

Ya ce wasu mammalakan defot masu zaman kansu sun kara farashin man daga N148 ga Lita zuwa N153-N155 tun Juma'ar da ta gabata.

Source: Legit.ng

Online view pixel