Harbi ya yawaita, matsanancin cunkoson titin a Onitsha bayan sojoji sun rufe dagar Niger

Harbi ya yawaita, matsanancin cunkoson titin a Onitsha bayan sojoji sun rufe dagar Niger

  • Wasu sojojin Najeriya sun rufe babbar gadar Niger wacce ke tsakanin garin Onitsha da Asaba yayin da mazauna Anambra ke sauraron sakamakon zaben
  • Har ila yau, an ji karar harbe-harben bindiga yayin da mazauna garin suka dinga gudun ceton rai a fadin garin duk da cunkoson da aka samu
  • Wannan lamarin yasa mutanen yankin ballantana matafiya suka tsaya a wurin cunkoson tare da sauka daga ababen hawansu

Anambra - An samu rikici tare da tashin-tashina a wuraren gadar Niger ta biyu da ke Onitsha bayan sojoji sun rufe dukkan bangarorin gadar tare da hana ababen hawa yawo.

Wakilin Legit.ng da ke kan hanyarsa ta zuwa Asaba tare da wasu fasinjoji ya sauko daga abun hawansa tare da yin tattaki zuwa dayan bangaren gadar domin cigaba da tafiye-tafiyen.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Bayan rugujewar gini, mummunar gobara ta kone gine-gine a Legas

Harbi ya yawaita, matsanancin cunkoson titin a Onitsha bayan sojoji sun rufe dagar Niger
Harbi ya yawaita, matsanancin cunkoson titin a Onitsha bayan sojoji sun rufe dagar Niger
Asali: UGC

A yayin wannan al'amarin ne, sojoji suka dinga harbi a iska domin tsarotar da matafiya wadanda suka harzuka da cunkoson kan titin.

An rufe titin ne bayan samu umarni daga sama

Wani matafiyi wanda ya bayyana sunansa da Obinna ya sanar da Legit.ng cewa sojoji sun yi ikirarin cewa sun rufe gadar ne sakamakon umarin da suka samu daga sama.

Harbi ya yawaita, matsanancin cunkoson titin a Onitsha bayan sojoji sun rufe dagar Niger
Harbi ya yawaita, matsanancin cunkoson titin a Onitsha bayan sojoji sun rufe dagar Niger
Asali: UGC

A yayin magana da harshen Ibo, ya ce:

"Sun ce gwamnatin tarayya ce ta umarcesu da su rufe titin har sai an kammala sanar da sakamakon zabe."
Obinna ya koka da cewa: "Ta yaya haka ya shafe mu? Wasu daga cikinmu za su wurare masu nisa ne kuma suke wahalar da mu kamar haka."

A dayar hanyar da ke kaiwa gadar Onitsa zuwa Asaba, sojoji sun tsare jama'a inda suka saka masu wucewa suna daga hannayensu sama.

Kara karanta wannan

Kano: Rayuka 5 sun salwanta, mutum 2 sun jigata a mummunan hatsarin mota

Masu babur din Achaba sun yi amfani da wannan damar wurin damawa. Sun dinga daukar fasinjojin da suka kagu da su gansu a inda ya dace, ballantana masu tafiya zuwa filin jirgi.

Daga farkon gadar zuwa karshen ta, 'yan achaba sun dinga karbar naira dari biyar domin fasinja da kayansa.

Ku biya mu kudinmu, Masu kada kuri'a sun bi wakilan jam'iyya domin karbar cin hanci

A wani labari na daban, daya daga cikin babbar matsalar da ke cigaba da haifar da matsala a Najeriya shi ne siyan kuri'a, wanda kuma ya cika a zaben gwamnan jihar Anambra.

Wakilan jam'iyyun siyasa da ke kare ra'ayoyin jam'iyuunsu an zargesu da bai wa masu kada kuri'a kudi daga dari biyar har zuwa dubu goma.

Kamar yadda Premium Times ta wallafa, an ga wani wakilin jam'iyya na ganawa da masu kada kuri'a bayan saka kuri'unsu tare da rubuta sunayensu a wata takarda, alamu da ke nuna za a biya su daga baya.

Kara karanta wannan

Matsolo ne, baya bani kuɗi: An kama matar aure da ta haɗa baki da gardawa 3 don garkuwa da mijinta

Asali: Legit.ng

Online view pixel