Gaskiya ta fito: ASUU ta magantu kan nadin da aka yi wa Dr Pantami na matsayin Farfesa

Gaskiya ta fito: ASUU ta magantu kan nadin da aka yi wa Dr Pantami na matsayin Farfesa

  • Kwamitin ASUU a jami'ar FUTO ta jihar Imo ta tabbatar da bincike kan nadin da aka yiwa Dr Pantami na farfesa a jami'ar
  • Kwamitin ya ce ya gamsu da nadin, duba da irin ka'idojin da aka bi wajen tabbatar da cancanta da kwarewa a wajen nadin
  • Hakazalika kwamitin ya ba da shawarar daukar mataki kan wadanda suka yi kokarin bata wa jami'ar suna baya nadin na Pantami

Imo - Kwamitin binciken kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ya wanke hukumomin jami’ar fasaha ta tarayya da ke Owerri (FUTO) daga cece-kucen da ake yi na nadin ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ibrahim Pantami, a matsayin Farfesa na Tsaron Intanet.

Jami'ar ta ce ta bi ka'idojin da suka dace kuma ta gabatar da wallafe-wallafen Pantami don tantancewa ga masu tantancewa na waje sannan kuma ta kafa ka'idar farko don nada shi Farfesa na Tsaron Intanet.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ceto malaman UNIAbuja da aka sace, an kama 'yan bindiga

Gaskiya ta fito: ASUU ta magantu kan nadin da aka yi Dr Pantami na matsayin Farfesa
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Kwafin rahoton mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin Farfesa MS Nwakaudu da wasu mambobi hudu ya bayyana irin matakan da jami'ar ta bi wajen nada Pantami Farfesa.

Daily Sun ta ruwaito rahoton na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Daga binciken da muka yi da shaidun da ke gaban kwamiti, mambobin na da ra’ayin cewa nadin Dr Isa Ibrahim a matsayin Farfesa a fannin tsaro ta Intanet ta hanyar Majalisar gudanarwa ta FUTO ta bi tsarin da ya dace.
"Kwamitin ya ba da shawarar ya kamata mahukuntan jami'ar cikin gaggawa su dauki matakan da suka dace, ciki har da na shari'a, a kan wadanda suka yi kokarin jawo zubar kima da martabar FUTO."

Rahoton ya yi nuni da cewa, sakamakon wasu kura-kurai da aka samu kan nadin Pantami a matsayin Farfesa a Makarantar Fasahar Bayanai da Sadarwa (SICT), kungiyar ASUU ta FUTO a ranar 22 ga Satumba, 2021 ta kafa kwamitin binciken.

Kara karanta wannan

Gwamnan Yobe zai gana da wasu jiga-jigan APC don dinke barakar APC a jihar Oyo

A cewar rahotanni, an ba da umarnin a cikin kwanaki bakwai a tabbatar ko an aiwatar da tsarin da ya dace wajen nadin Pantami a matsayin Farfesa na Tsaron Intanet ta Majalisar Mulki ta FUTO, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce shugaban SICT ya tantance wallafe-wallafen da ayyuka masu inganci ta amfani da ka'idojin FUTO na nadawa da habakawa kuma ya kafa ka'idar farko don a nada shi Farfesa na Tsaron Intanet.

Ya kara da cewa an gabatar da kaidar farko ga kwamitin tantance ma'aikata da kara girma (ASAPC-Professorial) kuma kwamitin ya tattauna batun tare da ba da shawarar hakan don amincewa daga majalisar FUTO.

Isa Pantami ya zama Farfesan Jami'a yana rike da kujerar Ministan Gwamnati a Najeriya

A wani labarin, Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, ya samu matsayi na Farfesa a harkar tsaron kafofin yanar gizo.

PR Nigeria tace Ministan ya na cikin mutane bakwai da suke matsayin mataimakin Farfesa da suka tsallaka zuwa Farfesa a jami’ar tarayya ta Owerri.

Kara karanta wannan

Gwamnan Legas ya kori daraktan kula da gine-gine bayan rugujewar bene mai hawa 22

Jami’ar fasahar FUTO da ke jihar Imo ta dauki wannan matakin ne a zama na 186 da ta yi wanda ya gudana a ranar Juma’a 20 ga watan Agusta, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel