Isa Pantami ya zama Farfesan Jami'a yana rike da kujerar Ministan Gwamnati a Najeriya

Isa Pantami ya zama Farfesan Jami'a yana rike da kujerar Ministan Gwamnati a Najeriya

  • Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya zama Farfesa a jami’ar tarayya da ke Owerri
  • Malamin na cikin wadanda aka tabbatar da karin matsayinsu a jami’ar FUTO
  • Ministan sadarwan kasar Farfesa ne yanzu a fagen tsaron kafafar yanar gizo

Abuja - Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, ya samu matsayi na Farfesa a harkar tsaron kafofin yanar gizo.

PR Nigeria tace Ministan ya na cikin mutane bakwai da suke matsayin mataimakin Farfesa da suka tsallaka zuwa Farfesa a jami’ar tarayya ta Owerri.

Jami’ar fasahar FUTO da ke jihar Imo ta dauki wannan matakin ne a zama na 186 da ta yi wanda ya gudana a ranar Juma’a 20 ga watan Agusta, 2021.

An yi wa Malamai hudu karin matsayi

Sauran manyan malaman da suka zama Farfesoshi a jami’ar sun hada da; Dr. Okechukwu Onyelucheya, Dr. Alex I. Opara, da Dr. Lawence Ettu.

Ragowar su ne; Dr. Conrad Enenebeaku, Dr. Chikwendu Okereke, da kuma Dr. Godfrey Emeghara.

Legit.ng Hausa tana da labari cewa Isa Ali Ibrahim Pantami mataimakin Farfesa ne a lokacin da yake jami’ar kasar Saudi Arabia daga 2014 zuwa 2016.

Isa Pantami ya zama Farfesan Jami'a yana rike da kujerar Ministan Gwamnati a Najeriya
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami Hoto: @MuhdAuwaal
Asali: Twitter

Ya aka yi Minista ya zama Farfesa?

A 2016 ne gwamnatin Muhammadu Buhari ta nada Dr. Pantami a matsayin shugaban hukumar NITDA. A Agustan 2019 ya samu kujerar Ministan tarayya.

Shafin Ministan na Research Gate ya bayyana cewa ya wallafa takardun bincike, nazarin ilmi, dakara wa juna sani da laccoci sama da 160 a kan fanninsa.

Wani malami a jami’ar ta FUTO ya shaida wa 'yan jarida cewa Ministan ba ya karbar albashi daga makarantar a halin yanzu, saboda gwamnati ta ba shi aiki.

Tuni masana harkar boko da masu sharhi suka fara magana a kan wannan karin matsayi da Ministan ya samu duk da ba ya karantar wa a wannan jami’a.

Kwanaki aka ji shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami wasu daga cikin Ministocinsa. Daga cikinsu akwai Ministan harkar noma, Alhaji Sabo Nanono.

‘Yan adawa a Majalisa sun ce wasan yara ake yi da aka yi waje da Ministocin. Hon. Ndudi Elumelu yace da haka, gara a shawo kan tsaro da tattalin arziki

Asali: Legit.ng

Online view pixel