Yadda fusatattun masu kada kuri'a suka garƙame ma'aikatan INEC a Anambra

Yadda fusatattun masu kada kuri'a suka garƙame ma'aikatan INEC a Anambra

  • Wasu mutane sun nuna fushinsu kan ma'aikatan INEC bayan kammala zaɓe ana tattara sakamako a karamar hukumar Orumba ta Arewa
  • Rahoto ya bayyana cewa ma'aikatan ne suka nemi barin cibiyar tattara sakamakon gundumar Oko II domin su koma ofishin INEC
  • Lamarin ya saitu ne bayan sojoji sun shiga lamarin, inda suka kwashe kayan aikin zabe masu muhimmanci zuwa ofis

Anambra - Fusatattun masu kaɗa kuri'a sun garƙame wasu daga cikin jami'an hukumar zaben mai zamanta kanta (INEC) ranar Asabar a Anambra.

Dailytrust tace lamarin ya faru a College Primary School, dake gundumar Oko II, karamar hukumar Orumba ta arewa.

A cewar ɗaya daga cikin sa ido a zaɓen, rikicin ya fara ne daga lokacin da ma'aikatan suka yi kokarin komawa cibiyar karban sakamakon karamar hukuma, su bar gunduman baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Soludo ya gagara saka kuri'a yayin da na'urar BVAS ta ki aiki

Zaben Anambra
Yadda fusatattun masu kada kuri'a suka garƙame ma'aikatan INEC a Anambra Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Meya kawo rikici tsakani?

Wata P.O mai aiki a runfar zabe, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin, tace mutane sun nemi a kammala karban sakamakon a gundumarsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarta su kuma ma'aikatan INEC suka ce an umarci sukai kayayyakin zaɓen ofishin INEC na ƙaramar hukumar saboda dare na yi.

Ta kuma kara da cewa hakan ne yasa mutane suka tada yamutsi kuma suka jaddadawa ma'aikatan cewa ba inda zasu je.

Tace:

"Domin hana ma'aikatan tafiya ne, masu kaɗa kuri'an suka garkame gate ɗin makarantar. Hakan ya kawo tashin hankali a cibiyar, duk da an turo yan sanda su gyara komai."

Ta ya aka shawo kan lamarin?

Rikicin bai lafa ba har sai sanda sojojin suka shiga tsakani, waɗan da suka zo daga hedkwatar ƙaramar hukuma suka ceci ma'aikatan

Daga nan kuma sojojin suka ɗauki kayayyakin zaɓe masu muhimmanci zuwa ofishin INEC na ƙaramar hukumar domin gudun abinda ka iya faruwa.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya yi basaja ya kai ziyaran bazata asibiti, ya damke ma'aikata na karban kudin Haram

A wani labarin kuma mun kawo muku cewa Yan bindiga sun sace akwatunan zabe a rumfunar zabe

Maharan sun sace akwatunan zabe guda biyu na zaben gwamnan Anambra da ke gudana a ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba.

Da isar su rumfunar zaben, sai yan bindigar suka fara harbi ba kakkautawa domin su tsorata masu zabe da jami'an tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel