Da duminsa: Soludo ya gagara saka kuri'a yayin da na'urar BVAS ta ki aiki

Da duminsa: Soludo ya gagara saka kuri'a yayin da na'urar BVAS ta ki aiki

  • Farfesa Charles Soludo ya bayyana damuwarsa kan yadda zaben jihar Anambra ke tafiyar hawainiya
  • Soludo, wanda shi ne dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar APGA, har yanzu ya kasa saka kuri'a saboda BVAS ba ya aiki a rumfar zabensu
  • Kamar yadda dan siyasan yace, an samu matsalar fasahar, babu jami'an tsaro kuma akwai karancin jami'an hukumar INEC a yankin da wasu sassan jihar

Charles Soludo, dan takarar gwamnan Anambra karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), har yanzu bai kada kuri'a ba.

Legit.ng ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan babban bankin Najeriyan ya isa rumfar zabensa da wuri amma ya kasa saka kuri'arsa saboda rashin aikin na'urar BVAS a wurin.

Da duminsa: Soludo ya gagara saka kuri'a yayin da na'urar BVAS ta ki aiki
Da duminsa: Soludo ya gagara saka kuri'a yayin da na'urar BVAS ta ki aiki
Source: UGC

Ya ce:

"Yanzu kusa karfe 12.30 kuma ba mu fara kada kuri'a ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Read also

Anambra 2021: Jiga-jigan al'amura 10 da ya dace a sani game da zaben gwamna

Dan takarar APGA din ya ce zai zanta da manema labarai bayan ya kada kuri'arsa cike da nasarar.

Kamar yadda rahoto ya bayyana, a lokacin, mutum tara kacal ne daga cikin sama da dari bakwai suka saka kuri'arsu a rumfar zaben.

Soludo ya kara da cewa:

"Mutane suna ta jiran su kada kuri'a tun kafin isowar jami'an INEC. A gaskiya fasahar BVAS kwata-kwata shirme ce.
"An fara kada kuri'a a wasu wurare, kuma a wuraren da aka fara, a kalla ana daukar minti ashirin kafin a tantance mutum daya.
"A gaskiya lamarin ya bani tsoro kuma a dukkan fadin jihar ne. Amma dai muna sa ran zai yi aiki. A cikin minti ashirin, masanin fasahar na'urar ya na ta duba ta.
"Na biyu kuwa shi ne rashin jami'an INEC a rumfunan zabe. Akwai matsalar tsaro. Babu dan sanda ko daya a nan, kuma hakan ne a duk fadin jihar."

Soludo ya jajanta yadda mutane suke ta tsaiko tare da jira tun karfe 7 na safe amma har wurin karfe 1 ba su saka kuri'a ba. Ya yi kira ga INEC da su gyara wannan fasahar.

Read also

Zaben Anambra 2021: Dalilai 4 da ka iya sa Charles Soludo na APGA ya lashe zabe

Zaben Anambra 2021: Dalilai 4 da za su iya sa Charles Soludo ya lashe zabe

A wani labari na daban, duk da akwai 'yan takara 18 tare da jerin jam'iyyun siyasa da suka fito gaba-gadi domin neman kujerar gwamnan jihar Anambra a zaben da za a yi ranar 6 ga watan Nuwamba, akwai 'yan takarar da babu shakka za a fafata da su.

Daga cikin 'yan takarar akwai Fafesa Charles Chukwuma Soludo, wanda shi ne dan takarar jam'iyya mai mulki a jihar ta All Progressives Grand Alliance (APGA).

Source: Legit.ng

Online view pixel