Zaben Anambra: Dan takaran APGA ya lashe zabe a kananan hukumomi 11 cikin 21 kawo yanzu

Zaben Anambra: Dan takaran APGA ya lashe zabe a kananan hukumomi 11 cikin 21 kawo yanzu

  • Dan takaran jam'iyyar APGA a zaben dake gudana yanzu haka a Anambra ya dau hanyar lashe zabe
  • Bisa sakamakon da aka tattara kawo yanzu a jihar, Farfesa Charles Soludo ke kan gaba kuma da tazara mai yawa
  • Daga shi sai dan takaran jam'iyyar PDP, sannan kuma na APC

Charles Chukwuma Soludo na jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ya lashe zaben kananan hukumomi goma sha daya kawo yanzu da ake cigaba tattara kuri'un da aka kada.

Kananan hukumomin sun hada da Awka South, Onitsha South, Orumba South, Anaocha, Anambra East, Njikoka, Orumba North, Aguwata, Oyi, Ayamelum, da Dunukofia.

Hukumar zabe ta kasa INEC ta sanar da cewa za'a cigaba da tattara sakamakon zaben ranar Lahadi.

Akwai kananan hukumomi 21 a jihar Anambra amma sakamakon 11 kadai aka sanar.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Soludo ne a sahun gaba, APGA ta lashe kananan hukumomi 16 a Anambra

Kawo yanzu, Charles Soludo na da jimillar kuri'u 74,859 daga kananan hukumomin 11, yayinda dan takaran PDP, Valentine Ozigbo na PDP ke biye da shi da kuri'u 30,581 sannan Andy Uba na APC mai kuri'u 26,056

Zaben Anambra: Dan takaran jam'iyyar APGA ya lashe zabe a kananan hukumomi shida
Zaben Anambra: Dan takaran jam'iyyar APGA ya lashe zabe a kananan hukumomi shida
Asali: Facebook

Ga jerin sakamakon:

Njikoka LGA

APC - 3,216

APGA - 8,803

PDP - 3,409

YPP - 924

Awka South

APC – 2595

APGA – 12891

PDP – 5489

Onitsha South LG

APC – 2050

APGA – 4281

PDP – 2253

Orumba South

APC: 2,060

APGA: 4,394

PDP: 1,672

YPP: 887

Anambra East LGA

APC 2034

APGA: 9746

PDP: 1380

Anaocha LGA

APC – 2085

APGA – 6911

PDP – 5,108

Orumba North

APC – 2692

APGA – 4826

PDP – 1863

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Soludo ya lashe karamar hukumar Anaocha, mahaifar 'yan takara uku

Aguwata

APC – 4773

APGA – 9136

PDP – 3798

Dunukofia

APC - 1991

APGA -4124

PDP - 1680

Oyi

APC - 2830

APGA - 6133

PDP - 2484

Ayamelum

APC - 2409

APGA - 3424

PDP - 2804

Asali: Legit.ng

Online view pixel