An Shiga Tashin Hankali bayan Kashe Shugaban Al'umma, Matasa Sun Kona Gidan Sarki a Najeriya

An Shiga Tashin Hankali bayan Kashe Shugaban Al'umma, Matasa Sun Kona Gidan Sarki a Najeriya

  • ’Yan sanda sun kama mutum bakwai bisa zargin hannu a kisan shugaban ƙauyen Odoro Ikot 1 da kona gidan basarake
  • An zargi wani mutum mai suna Ifiok Akpan da daba wa marigayin wuka a ciki yayin takaddama kan rabon gado
  • Rundunar yan sanda ta ce an kai gawar wanda aka kashe zuwa asibiti domin gudanar da binciken gawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom - An shiga yanayi na tashin hankali a kauyen Odoro Ikot 1 da ke masarautar Ukana Mbak Ikot, a ƙaramar hukumar Essien Udim ta jihar Akwa Ibom, bayan kisan gillar da aka yi wa shugaban ƙauyen, Mista Ukeme Jonah.

Rahotanni sun nuna cewa bayan kashe shugaban al'ummar kauyen, an kuma kona gidan basaraken yankin da motarsa.

Yan sanda.
Jami'an rundunar yan sandan Najeriya a cikin shirin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Leadership ta ruwaito cewa rundunar ’yan sandan jihar Akwa Ibom ta kama mutum bakwai bisa zargin hannu a kisan da kuma lalata kadarorin Sarkin ƙauyen, Cif Akpan Brown.

Kara karanta wannan

Shugaban INEC ya tafi ƙasar waje, ya faɗa wa duniya matakin da za su ɗauka kan takarar Atiku a 2027

Yadda aka kashe shugaban kauye

Lamarin ya faru ne a ranar 2 ga Nuwamba, 2026, a ƙauyen Ukana Mbak Ukot da ke yankin Odoro Ikot, kuma an kai rahotonsa ga ’yan sanda washegari.

A cewar ’yan sanda, binciken farko ya nuna cewa an samu saɓani tsakanin Ifiok Akpan, mai shekara 42, da marigayin kan rabon kuɗin iyali.

Rahotanni sun ce a lokacin takaddamar, Akpan ya daba wa Jonah wuka a cikinsa da kwalbar gilashi da ta fashe. An garzaya da wanda aka yi wa rauni zuwa asibiti, amma daga bisani ya rasu sakamakon raunukan da ya samu.

An ƙona gidan basarake

Bayan mutuwar Jonah, an kai gawarsa zuwa gidan basaraken ƙauyen, inda wasu mutane suka ƙone gidan da motarsa ƙirar Toyota 4Runner a matsayin ramuwar gayya, kamar yadda rahotanni suka nuna..

Wani mazaunin yankin da ya fusata, Anietie Udoma, ya ce wasu matasa sun yi zargin cewa basaraken na da hannu a kisan, saboda an gano gawar shugaban ƙauyen a harabar gidansa.

Kara karanta wannan

Hatsabibin ɗan bindiga da ya addabi jama'a ya sheƙa barzahu a Katsina

Udoma ya ce:

“Sun zo ne domin su kashe basaraken, saboda sun yi imanin cewa shi ne ya shirya mutuwar shugaban ƙauyen, tun da an gano gawarsa a harabar gidansa.”

Da ya fahimci cewa rayuwarsa na cikin haɗari, basaraken ya gudu daga gidan, kafin matasan su cinna wa gidansa da motarsa wuta.

Akwa Ibom.
Taswirar jihar Akwa Ibom da ke Kudu maso Kudancin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

’Yan sanda sun kama mutane bakwai

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Timfon John, ta ce jami’an rundunar sun kama Akpan a maboyarsa, yayin da aka cafke wasu mutane shida a wani samame da aka gudanar a wurin da lamarin ya faru a ranar 3 ga Nuwamba.

John ta ce ana tsare da mutanen bakwai a hannun ’yan sanda, yayin da aka ajiye gawar marigayin a ɗakin ajiye gawa domin gudanar da binciken gawar.

Matasa sun yi arangama a Kaduna

Kun ji cewa an shiga fargaba bayan wasu gungun matasa masu hamayya da juna sun yi arangama a unguwannin Kwaru da Unguwar Yero da ke karamar hukumar Kaduna ta Arewa a jihar Kaduna.

Rikicin, wanda rahotanni suka ce ya jikkata wasu mutane, ya samo asali ne daga rashin jituwa tsakanin matasan unguwannin biyu kusan mako guda da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262