Matashi ya ga tsohon Malaminsa ya talauce babu aiki, ya mayar da shi Miloniya cikin kwana 3

Matashi ya ga tsohon Malaminsa ya talauce babu aiki, ya mayar da shi Miloniya cikin kwana 3

  • Wani matashi dake fafutukar neman halaliyarsa ya yi kicibis da wani dattijo yana kwana cikin mota a bakin titi
  • Da ya kusanci dattijon sai ya gano cewa tsohon Malaminsa ne wanda ya rasa muhallinsa da aikin sa sakamakon annobar Korona
  • Tsohon dalibin ya taimakawa tsohon Malaminsa kuma ya kama masa Otal kuma ya roki mutane su taimaka masa

Amurka - Wani Malami ya shiga halin talauci da kunci bayan rasa aiki da muhallinsa sakamakon annobar Korona da ta bulla a duniya a shekarar 2020.

Goal Cast ta ruwaito cewa wani matashi mai suna Steve Nawa ya gano wani dattijo yana kwana cikin mota yayinda yake hanyar tafiya aiki.

Kawai sai ya kusanci mutumin amma abin mamaki sai ya ga Jose Villaruel, tsohon Malaminsa ne a kasar Amurka.

Read also

Babban magana: Wasu mutane 2 masu sana'ar tura amalanke sun mutu yayin faɗa kan N200 kacal

Matashi ya ga tsohon Malaminsa ya talauce
Matashi ya ga tsohon Malaminsa ya talauce babu aiki, ya mayar da Miloniya cikin kwana 3 Hoto: Goalcast
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon Malaminsa ya talauce gaba daya

Steve ya tattauna da Mr Villaruel inda ya fahimci halin da tsohon Malaminsa ke ciki tun bayan annobar Korona.

Dattijon ya bayyana masa cewa hanya daya tilo da yake samun kudi wani tallafin gwamnati ne kuma matarsa dake rashin lafiya a Mexico yake turawa kudin.

Steve ya canza rayuwar tsohon Malaminsa

Rahoton ya bayyana cewa kai tsaye Steve ya dauke Malaminsa daga kan titi kuma ya kama masa dakin Otal kuma ya bashi kyautan $300 (N123,846).

A riwayar News Yahoo, dalibin ya garzaya kafar Intanet ya kafa shafin GoFundMe kuma ya samu nasarar mutane suka hadawa tsohon Malaminsa $15,000 (N6,192,300).

Bayan gudunmuwan da mutane suka bada, an tarawa mutumin $27,000 (N11,146,140) cikin kwanaki uku.

Gwamna Zulum zai gwangwaje malaman makaranta da ƙarin Albashi a jihar Borno

Read also

So makaho: Matashi ya fada soyayyar 'yar fim da ta girme shi, ya daina cin abinci saboda begenta

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya sha alwashin fara biyan malaman makarantun firamare mafi karancin albashi na N30,000, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau, ya fitar ranar Talata, Zulum ya koka kan yadda wasu malamai ke karɓar N11,000 a ƙarshen wata.

Gusau ya bayyana cewa mai gidansa ya ɗauki wannan alƙawarin ne a gidan gwamnati dake Maiduguri, yayin da yake kaddamar da shugabannin hukumar bada ilimin bai ɗaya ta jihar Borno.

Source: Legit.ng

Online view pixel