Gwamna Zulum zai gwangwaje malaman makaranta da ƙarin Albashi a jihar Borno

Gwamna Zulum zai gwangwaje malaman makaranta da ƙarin Albashi a jihar Borno

  • Gwamna Zulum na jihar Borno ya yi alƙawarin karawa malaman makaranta albashi a jihar Borno
  • Zulum yace abin takaici ne yadda malaman makaranta ke fama da karancin walwala da kulawa daga gwamnati
  • Ya yi alƙawarin fara biyan mafi karancin albashi na N30,000 ga malaman da aka tantance suna da kwarewar koyarwa

Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya sha alwashin fara biyan malaman makarantun firamare mafi karancin albashi na N30,000, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau, ya fitar ranar Talata, Zulum ya koka kan yadda wasu malamai ke karɓar N11,000 a ƙarshen wata.

Gusau ya bayyana cewa mai gidansa ya ɗauki wannan alƙawarin ne a gidan gwamnati dake Maiduguri, yayin da yake kaddamar da shugabannin hukumar bada ilimin bai ɗaya ta jihar Borno.

Read also

Gwamnonin kudu sun gana a jihar Legas, Sun cimma matsaya kan abubuwa da dama

Gwamna Babagana Zulum
Gwamna Zulum zai gwangwaje malaman makaranta da ƙarin Albashi a jihar Borno Hoto: ripplesnigeria.com
Source: UGC

Hukumar ta samu sabbin shugabanni biyo bayan ƙarewar wa'adin tsaffin shugabannin na UBE.

Menene matsalar malaman Firamare?

Vanguard ta rahoto cewa a jawabin Zulum na wurin taron yace:

"Ɗaya daga cikin matsalan dake damun ilimin firamare yau shine rashin kula da jin daɗin malamai. Abin takaici ne har yanzin akwai masu karbar albashin N11,000 ko N13,000."
"Ina mai tabbatar muku duk da ƙalubalen tattalin arziki da muke fama da shi, muna kokarin duk wani malami da ya cike sharuɗɗa ya rika karbar N30,000, wanda shine mafi ƙaranci a ƙasa."

Wane mataki za'a ɗauka kan malaman da ba su dace ba?

Gwamnan yace malaman da aka gano ba su da kwarewa bayan gudanar da jarabawa, za'a tura su makarantun horad da malamai domin su samu dabarun kiyarwa.

Read also

Dubun wasu Lakcarori biyu dake neman ɗalibai mata da biɗala ya cika, An sallamesu daga aiki

Hakanan kuma waɗanda ba su yi karatu ba kwata-kwata za'a maida su ma'aikatan da ba malamai ba a makarantu.

A wani labarin kuma Gwamnonin Kudu sun bukaci shahararren malami a Najeriya ya daina caccakar Shugaba Buhari

Gwamnonin yankin kudu maso gabas sun roki shahararren malamin nan na addinin kirista, Rabaran Ejike Mbaka, ya daina magana mara ɗaɗi akan shugaban ƙasa Buhari.

Shugaban gwamnonin yankin, Gwamna David Umahi, tare da rakiyar gwamna Ifeanyi Ugwuanyi, na jihar Enugu , sune suka roki malamin amadadin sauran.

Source: Legit.ng

Online view pixel