Babban magana: Wasu mutane 2 masu sana'ar tura amalanke sun mutu yayin faɗa kan N200 kacal

Babban magana: Wasu mutane 2 masu sana'ar tura amalanke sun mutu yayin faɗa kan N200 kacal

  • Wasu masu tura amalanke sun yi fada a kasuwar Aba, jihar Abia har ta kai ga sun rasa rayyukansu
  • Shaidan gani da ido ya ce sun fara rikici ne saboda wani kaya da za a dauka wa wani dan kasuwa ya biya N200
  • Daya daga cikin masu amalanken ya yi wa abokin aikinsa rauni da wuka hakan ya yi sanadin mutuwarsa, shi kuma mutane suka halaka shi

Jihar Abia - Wani rikici mai zafi tsakanin wasu mutane biyu masu tura amalanke ya yi sanadin rasuwar mutanen biyu a birnin Aba a ranar Talata, The Nation ta ruwaito.

Rundunar yan sandan jihar Abia ta tabbatar da afkuwar lamarin inda ta ce rikici ne ya shiga tsakaninsu har ta kai daya daga cikin masu tura amalanken ya kashe daya.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan sintiri sun yi ram da mutumin da ke bayyana wa mata al'aurarsa

Babban magana: Wasu mutane 2 masu sana'ar tura amalanke sun mutu yayin faɗa kan N200 kacal
Wasu mutane 2 masu sana'ar tura amalanke sun mutu yayin faɗa kan N200. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin yan sandan jihar Abia, SP Geoffrey Ogbonna, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai NAN a Aba a ranar Laraba cewa fusatattun mutane sun halaka daya daga cikin masu fadan bayan ya kashe abokin aikinsa.

Rahoton The Nation ya ce Ogbonna ya gargadi mutane su guji daukan doka a hannunsu idan rashin jituwa ya shiga tsakani.

Ya ce yan sanda sun kwashe gawarwakin masu tura amalanken sun kai wurin ajiyar gawa a asibiti.

Shaidan gani da ido ya magantu kan yadda abin ya faru

Wani ganau ya shaidawa manema labarai cewa a safiyar ranar Talata ne masu tura amalanken suka fara rikici kan wanda zai dauki kayan da wani dan kasuwa ya siya a kasuwan kusa da makabarta a Aba, Abia.

Ya ce mazan biyu sun yi mummunar fada da muggan makamai suka yi wa juna rauni kan N200 da za a biya idan sun taimakawa dan kasuwar daukan kayansa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wani gini mai hawa-hawa ya sake ruftawa a jihar Legas

Majiyoyi sun ce mutane sun yi kokarin raba fadan amma masu amalanken sun ki sauraron rokon mai kayan da sauran mutane da ke kokarin yin sulhu.

Shaidan ya ce daya daga cikin masu amalanken ya dabawa dayan wuka a ciki, wuya sa wasu sassan jikinsa yayin fadan, hakan ya yi sanadin mutuwarsa.

A cewarsa, da ya lura cewa dayan mai amalanken ya mutu, ya yi kokarin tserewa amma mutane suka tare shi suka kashe shi nan take.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel