Daga karshe: Atiku ya bayyana dalilin da yasa ya yi aure daga wasu kabilu a Najeriya

Daga karshe: Atiku ya bayyana dalilin da yasa ya yi aure daga wasu kabilu a Najeriya

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce ‘yan Najeriya sun fi kyau a tare duk da zurfafawar kabilanci da addin da ke kasar
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriyar ya ce ana iya samun hadin kai ne ta hanyar yarda da juna da hakuri da juna
  • Atiku ya kuma ce bisa kokarinsa na auran mata daga sassan kasar nan, ‘ya’yansa suna da ‘yan’uwa maza da mata daga bangarori daban-daban

Kaduna - Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar ya bayyana dalilin da ya sa ya auri mata daga yankuna daban-daban na Najeriya.

Atiku yayin da yake gabatar da jawabinsa a Arewa House a ranar Alhamis, 4 ga watan Nuwamba, ya ce hadin kan Najeriya ya kamata ya zama karbabbe; yarda da cewa kowa daya ne kuma jama'a daya ne masu manufa guda - Najeriya.

Read also

Ministan Buhari: Ya kamata gwamnati ta daina yin sabbin tituna a Najeriya bisa wasu dalilai

Daga karshe: Atiku ya bayyana dalilin da yasa ya yi aure daga wasu kabilu a Najeriya
Atiku Abubakar | Hoto: bbc.com
Source: Facebook

A cikin jawabinsa mai taken; ‘Unity in Diversity' Atiku ya ce a tsawon rayuwarsa bai taba kallon ‘yan Najeriya a matsayin mutane daban-daban ba.

A cewar tsohon mataimakin shugaban kasar, duk ’yan Najeriya daya ne kuma duk lokacin da ya ga dan Najeriya dan kabilar Yarbawa ko Hausawa ko Igbo ganin dan Najeriya yake masa tare da fatan alheri a gare shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Atiku ya ce:

"Shi ya sa ban zabi waye ko kuma daga ina zan yi aure ba, na auri mata masu bambancin al'adu domin bana duba tarihinsu, sai dai kawai ina ganinsu a matsayin mata 'yan Najeriya.
"'Ya'yana suna da 'yan'uwa maza da mata daga wurare daban-daban. Shi ya sa nake da yakinin cewa za a iya samun hadin kai mai karfi a Najeriya saboda na sanya hakan ya faru a cikin iyalina."

Read also

Gwamna ya bayyana shirin PDP, ya ce ta shirya ceto Najeriya daga mummunan shugabanci

A wajen Atiku ma’anar hadin kai ga masu mabambantan ra’ayi shi ne zaman lafiya da hakuri da juna duk da sabanin da ke tsakanin al’umma.

Ya ce a yanzu ya zama dole 'yan Najeriya su hada kai, su so juna su kuma yi hakuri da junansu.

Ya kuma bayyana cewa, nuna wariya shi ke jawo duk wasu matsaloli da ke addabar al'ummar kasar, musamman a cikin wadannan shekarun.

Lauya ya fadi abubuwa 4 da suka sa kundin tsarin mulkin Najeriya ya zama matsalar kasar

A wani labarin, Olanipekun a ranar Laraba, 3 ga watan Nuwamba, ya ce mafi girman kundin doka a Najeriya yaudara ce kuma zunzurutun karya.

Vanguard ta rahoto cewa, lauyan masanin tsarin mulki ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da takarda a taro karo na 13 na jami’ar Redeemer mai taken, “Beyond the Pandemic: Createing a new normal”.

Ya ce kundin tsarin mulkin ya tara dukkan hukumomin tsaro a gwamnatin tarayya da duk wani sanannen tsarin mulki a duniya.

Read also

Bayan lashe zabe, sabon shugaban matasan PDP ya magantu kan manufarsa akan APC

Source: Legit.ng

Online view pixel