Ministan Buhari: Ya kamata gwamnati ta daina yin sabbin tituna a Najeriya bisa wasu dalilai

Ministan Buhari: Ya kamata gwamnati ta daina yin sabbin tituna a Najeriya bisa wasu dalilai

  • Ministan ayyuka da gidaje a Najeriya ya bayyana bukatar dakatar da ayyukan sabbin tituna
  • A cewarsa, halin da kasar ke ciki ba daidai bane kasar take kara taro sabbin ayyukan tituna a cikinta
  • Ya kuma bukaci gwamnati ta sake nemo hanyoyin samun kudin shiga saboda rage cin bashi

Abuja - Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, Babatunde Fashola, ministan ayyuka da gidaje a Najeriya, ya ce kasar ba ta bukatar sabbin ayyukan tituna a yanzu.

Ministan ya yi magana ne a ranar Laraba lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai kan ayyukan kare kasafin kudin ma’aikatar.

Fashola ya ce maimakon bayar da sabbin ayyukan tituna, ya kamata a yi amfani da “iyakantattun albarkatu” wajen kammala ayyukan da aka yi watsi da su da kuma wadanda ba a kammala ba.

Kara karanta wannan

Shugaban NDLEA: Ba kudi a hukumar NDLEA, daga gidana na dauko TV zuwa ofis

Ministan Buhari: Ya kamata gwamnati ta daina yin sabbin tituna a Najeriya bisa wasu dalilai
Ministan Buhari, Babatunde Fashola | Hoto: dailypost.ng
Asali: Depositphotos

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yawancin ayyukan na karuwa kuma dukkanmu dole ne mu nemo hanyar da za mu bi don cimma matsaya daya saboda kudaden shigar da muke samu ba sa karuwa daidai gwargwado."

Fashola ya kuma koka da cewa yayin da ake kara bullo da wasu ayyukan tituna, ma’aikata da kason da ake baiwa ma’aikatarsa sun kasance kamar yadda suke a baya, Punch ta ruwaito.

Ya kuma bukaci ‘yan majalisar dokokin kasar da su amince da rage bukatunsu na gyaran tituna a karkashin shirinsu na shiyya da aka fi sani da ayyukan mazabu.

Bayan bayyana dalilansa, ministan ya yi tsokaci kan mafiya, inda ya ce.

“Idan ‘yan majalisa daga kowace jiha za su iya haduwa su ce, wannan aikin ya fi muhimmanci, kuma mu yanke shawarar cewa mu matsar da aikin shiyya-shiyya – mu ce abin da muke so mu samu ke nan – wannan tattaunawa ce ta gaskiya dole ne mu yi. ”

Kara karanta wannan

Bayan lashe zabe, sabon shugaban matasan PDP ya magantu kan manufarsa akan APC

Ministan ya kuma ce dole ne gwamnati ta kara samar da kudaden shiga domin rage rance, ya kara da cewa irin wadannan basussuka sun zama abin damuwa a Najeriya.

Gwamnan Legas ya kori daraktan kula da gine-gine bayan rugujewar bene mai hawa 22

Jaridar The Naation ta ruwato cewa, gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya dakatar da babban manajan hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas (LASBCA) Gbolahan Oki.

Gwamnan ya sha alwashin gano abin da ya faru tare da hukunta wadanda ake tuhuma da hannu a rugujewar bene mai hawa 22 da ya ruguje a Ikoyi ta jihar.

Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai da Dabaru Gbenga Omotoso, ya fitar, ta ce gwamnatin jihar za ta kafa wani kwamiti mai zaman kansa da zai binciki rugujewar ginin na kan titin Gerrard, Ikoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel