Lauya ya fadi abubuwa 4 da suka sa kundin tsarin mulkin Najeriya ya zama matsalar kasar

Lauya ya fadi abubuwa 4 da suka sa kundin tsarin mulkin Najeriya ya zama matsalar kasar

Babban Lauyan Najeriya, Cif Wole Olanipekun, ya bayyana kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima a matsayin zunzurutun karya, kuma takardar da ba ta dace ba da ke bukatar canji ba gyara ba.

Olanipekun a ranar Laraba, 3 ga watan Nuwamba, ya ce mafi girman kundin doka a Najeriya yaudara ce kuma zunzurutun karya.

Vanguard ta rahoto cewa, lauyan masanin tsarin mulki ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da takarda a taro karo na 13 na jami’ar Redeemer mai taken, “Beyond the Pandemic: Createing a new normal”.

Ya ce kundin tsarin mulkin ya tara dukkan hukumomin tsaro a gwamnatin tarayya da duk wani sanannen tsarin mulki a duniya.

Lauya ya nuna abubuwa 4 da suka sa kundin tsarin mulkin 1999 ya zama matsalar Najeriya
Cif Wole Olanipekun | Hoto: Wole Olanipekun
Source: Facebook

Olanipekun ya yi gargadin cewa gyara kundin tsarin mulkin kamar yadda yake a halin yanzu zai dagula al’amura saboda takardar ba ta da wani amfani ko kuma gaskiya a cikinta.

Read also

Ministan Buhari: Ya kamata gwamnati ta daina yin sabbin tituna a Najeriya bisa wasu dalilai

Da yake karin haske kan wasu matsalolin da ke tattare da kundin, babban lauyan ya ce tanadin sashe na 224(1) na kundin tsarin mulkin kasar da ya tanadi tsarin samar da ‘yan sanda daya kacal ga kasar da gwamnati ke iko da ita a cibiyar ba gaskiya ba ne kuma karya not kawai.

A cewar Olanipekun, kundin tsarin mulkin kasar baki dayansa baya wakiltar duk wani abu sahihi da na gaskiya.

1. Tsarin aikin 'yan sanda

Dangane da yawa da girman Najeriya, Olanipekun ya yi gargadin cewa tsarin ba zai iya tsare Najeriya yadda ya kamata ba ta tsarin samar da 'yan sanda na bai daya.

Ya yi kira da a rarraba tsarin tsaro a Najeriya domin a samu damar dakile ayyukan masu aikata laifuka yadda ya kamata.

Read also

Fadin gaskiya ne ya jawo ake hantarar Shugaban Majalisar Dokokin Filato - Dan majalisa

2. Majalisar Dokoki ta kasa da gyaran kundin tsarin mulkin da ake hasashen

Wani misali a cewar babban lauyan shi ne, girman kan da majalisar dokokin kasar ta nuna na shirin yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulki ba tare da wani sanannen marubuci ba ko makamancin haka ba.

Da yake nakalto kalaman Peter Drucker, Olanipekun ya ce a halin da ake ciki yanzu, babu wani abu mara amfani kamar yin wani abu wanda bai kamata a yi ba.

3. Rusa tsarin tarayya na yanzu

Babban lauyan a yayin da yake kokawa kan yadda ake tattara madafun iko a kasar ya ce abin da Najeriya ke bukata a halin yanzu shi ne ruguje na tsarin tarayya.

Olanipekun ya ce kamata a dauki irin wannan mataki tare da fahimtar bangarori daban-daban na Najeriya da ke da banbanci.

Ya ce kasar a yin hakan ne za ta koyi darasi daga sauran kasashe, yadda za a sarrafa, gudanar da kuma yin aiki tare da wadannan bangarori daban-daban tare da sabon kundin tsarin mulki.

Read also

Ba ni da hannu a dirar mikiya da jami'an tsaro suka yi a gidan Mary Odili, Malami

4. Yadda ake bautar da jihohi a Najeriya

Olanipekun a lokacin da yake magana game da ayyukan gwamnati a matakin jiha ya ce jihohin tarayya sun zama bayi ga gwamnatin tarayya.

Ya ce a yunkurin da Najeriya ke yi na gudanar da tsarin mulkin shugaban kasa irin na Amurka, tsarin tarayya a Najeriya ya zama kamar alakar ubangida da bayi.

Ya ce gwamnoni a fadin jihohinsu an sa su nuna kansu a matsayin manyan jami’an tsaro na jihohinsu alhalin a hakikanin gaskiya ba su da iko a kan kowane tsari na tsaro ko hukuma.

Ministan Buhari: Ya kamata gwamnati ta daina yin sabbin tituna a Najeriya bisa wasu dalilai

A wani labarin, Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, Babatunde Fashola, ministan ayyuka da gidaje a Najeriya, ya ce kasar ba ta bukatar sabbin ayyukan tituna a yanzu.

Ministan ya yi magana ne a ranar Laraba lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai kan ayyukan kare kasafin kudin ma’aikatar.

Read also

Gwamnatin Buhari ta amince da biyan kudin kammala titin Gombe zuwa Biu

Fashola ya ce maimakon bayar da sabbin ayyukan tituna, ya kamata a yi amfani da “iyakantattun albarkatu” wajen kammala ayyukan da aka yi watsi da su da kuma wadanda ba a kammala ba.

Source: Legit.ng

Online view pixel