Yanzu-yanzu: Ƙungiyar IPOB ta saduda, ta soke dokar zaman gida na dole, ta ce a fita a yi zaɓe a Anambra

Yanzu-yanzu: Ƙungiyar IPOB ta saduda, ta soke dokar zaman gida na dole, ta ce a fita a yi zaɓe a Anambra

  • Kungiyar IPOB mai neman kafa kasar Biafra ta soke dokar tilastawa mutane zaman gida da ta saka a kudu maso gabas
  • IPOB ta soke dokar ne ana kwana biyu kafin yin zaben gwamnan jihar Anambra wadda a baya ta ce ba za a yi ba sai an sako Nnamdi Kanu
  • A wani abu mai kama da mi'ara koma baya, IPOB ta soke dokar ta bukaci mutanen Anambra su fita su yi zabe ta tare da fargaba ba

Haramtaciyyar kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) ta soke dokar da ta saka na zama gida na dole a yankin kudu mazo gabas, rahoton The Cable.

Haramtaciyyar kungiyar ta yi barazanar hana harkoki baki daya a yankin kudu maso gabas din daga ranar 5 ga watan Nuwamba.

Yanzu-yanzu: Kungiyar IPOB ta saduda, ta soke dokar zaman gida na dole, ta ce a fita a yi zabe a Anambra
Kungiyar IPOB ta saduda, ta soke dokar zaman gida na dole, ta ce a fita a yi zabe a Anambra. Hoto: The Nation
Source: Twitter

Read also

Miyagu na amfani da sunan IPOB suna kashe bayin Allah da basu ji ba basu gani ba – Gwamnonin kudu maso gabas

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hakan na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya ta tura jami'an tsaro da dama jihar ta Anambra yayin da ake shirin yin zaben a ranar Asabar.

Haramtaciyyar kungiyar ta yi barazanar hana harkoki baki daya a yankin kudu maso gabas din daga ranar 5 ga watan Nuwamba.

A baya kungiyar ta yi barazanar cewa ba za a yi zabe a jihar Anambra har sai an sako shugabanta Nnamdi Kanu.

Emma Powerful, Kakakin IPOB, a ranar Alhamis, ya ce an dage dokar na zaman gida dole domin bawa mutanen jihar Anambra daman fita su kada kuri'a a zaben gwamna da za a yi a ranar Asabar.

Ya ce:

"Mutanen jihar Anambra su fita kwansu da kwarkwata kuma cikin lumana su kada kuri'unsu a ranar 6 ga watan Nuwamban 2021, su zabi shugaban da suke ra'ayi kuma kada su yarda wani mutum ko kungiya ko jami'an tsaro ya musu barazana."

Read also

Gwamnonin kudu maso gabas za su sa labule da Shugaba Buhari kan Nnamdi Kanu

Powerful ya kara da cewa ba za a lamunci magudin zabe ba don haka dole a yi zabe sahihi kuma na adalci.

Ya kuma yi kira ga yan Biafra, Kungiyar IPOB da abokanan Biafra da masu kaunar yanci su cigaba da goyon bayan fafutikar da suke yi na neman kafa kasarsu.

Soke dokar ba ragwanci bane, Emma Powerful

Daga karshe ya ce soke dokar zaman gidan na dole ba ragwanci bane, kawai dai IPOB na fatan dattawa, shugaban addini da masu ruwa da tsaki da suka saka baki za su tabbatar an sako Nnamdi Kanu.

Source: Legit.ng

Online view pixel