Miyagu na amfani da sunan IPOB suna kashe bayin Allah da basu ji ba basu gani ba – Gwamnonin kudu maso gabas

Miyagu na amfani da sunan IPOB suna kashe bayin Allah da basu ji ba basu gani ba – Gwamnonin kudu maso gabas

  • Gwamonin kudu maso gabas, sun bayyana cewa yan kungiyoyin asiri, yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane da amfani da sunan IPOB don aikata laifuka a yankin
  • Kungiyar gwamnonin yankin ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro a kan su kare rayukan al'umman jihar Anambra gabannin zaben gwamna da za a yi a ranar Asabar mai zuwa
  • Gwamnonin sun kuma yi wa al'umman jihar Anambra fatan yin zabe cikin lumana

Anambra - Kungiyar gwamnonin kudu maso gabas ta bayyana cewa miyagu na amfani da sunan kungiyar yan awaren IPOB wajen kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba, jaridar Punch ta rahoto.

Kungiyar ta bayyana hakan ne yayin da take kira ga hukumomin tsaro a kan su kare rayukan al'umman jihar Anambra gabannin zaben gwamna da za a yi a ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba.

Read also

Gwamnonin kudu maso gabas za su sa labule da Shugaba Buhari kan Nnamdi Kanu

Miyagu na amfani da sunan IPOB suna kashe bayin Allah da basu ji ba basu gani ba – Gwamnonin kudu maso gabas
Miyagu na amfani da sunan IPOB suna kashe bayin Allah da basu ji ba basu gani ba – Gwamnonin kudu maso Mazi Nwonwu
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga gwamnan jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, David Umahi, a ranar Alhamis, 4 ga watan Nuwamba, Vanguard ta kuma rahoto.

Sanarwar ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Muna rokon dukkanin hukumomin tsaro da aka tura don zaben Anambra da su yi wa Allah su kare rayukan mutanenmu a jihar Anambra yayin da suke aiwatar da ayyukansu bisa doka.
"Muna sane da cewar rashin tsaro da ke kudu maso gabas ya fi gaban IPOB. Yan kungiyoyin asiri, barayi da masu garkuwa da mutane suna amfani da sunan IPOB don kashe-kashen bayin Allah da basu ji ba basu gani ba. ba za mu bari wannan ya ci gaba ba.
"Muna godiya ga gwamnatin tarayyar Najeriya da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta kan jajircewar da suka yi na gudanar da zaben Anambra a ranar 6 ga watan Nuwamba, 2021. Za mu ba su dukkan goyon bayan da suke bukata kuma za mu taimaka musu wajen ganin an gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci da lumana. Saboda haka, muna kira ga jama’ar mu da su fito su zabi ‘yan takarar da suke so domin an tabbatar mana da cewar za a samar da isassun matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyinsu.

Read also

Rashin tsaro: Gwamnatin Zamfara ta hukunta mutane sama da 1, 000 da suka saba doka

"Muna da yakinin cewa ta hanyar tattaunawarmu, cewa shugabannin addini, ohaneze Ndigbo da sarakunan gargajiya, IPOB za su ga dalilai na dakatar da dokar zaman gida ciki harda na ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba 2021.
"Mu a matsayinmu na gwamnonin kudu masu gabas, mun jajirce domin samar da mafita kan halin da ake ciki a kudu maso gabas kuma za a cimma hakan cikin sauri idan aka dakatar da dokar zaman gida da duk rikici a kudu maso gabas.
"Muna yiwa mutanen Anambra fatan gudanar da zabe lafiya a ranar 6 ga Nuwamba 2021."

Gwamnonin kudu maso gabas za su sa labule da Shugaba Buhari kan Nnamdi Kanu

A baya mun kawo cewa kungiyar gwamnonin kudu maso gabas ta bayyana cewa za ta gana da gwamnatin tarayya kwanan nan kan lamarin shugaban yan kungiyar awaren IPOB, Nnamdi Kanu.

Kungiyar ta bayyana cewa ganawar za ta tabbatar da ganin cewa an yi amfani da mafita na siyasa a kan lamarin Kanu wanda ke tsare a hannun rundunar tsaro ta farin kaya, rahoton Punch.

Read also

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun bindige jami’an yan sanda 4 a jahar Anambra

Hakazalika, taron zai magance rikicin da ake fama da shi a yankin kudu maso gabas da kuma dokar zaman gida da kungiyoyin masu fafutuka daban-daban suka kafa, ruwayar Pulse Nigeria.

Source: Legit.ng

Online view pixel