Katsina: Jami'an kwastam sun yi ram da matashi dauke da sunki 230 na hodar Iblis

Katsina: Jami'an kwastam sun yi ram da matashi dauke da sunki 230 na hodar Iblis

  • Jami'an hukumar kwastam, reshen jihar Katsina, sun yi ram da matashi dauke da sunki 230 na hodar Iblis
  • An kama Saifullahi a garin Shargalle kan babban titin Daura zuwa Katsina a karamar hukumar Mashi ta jihar
  • Ya bayyana cewa, wannan ne karo na uku da ake bashi dakon kaya daga Legas zuwa Katsina ba tare da ya san hodar Iblis bace

Katsina - Hukumar kwastam ta kasa, NCS, reshen jihar Katsina, ta damke wani mai suna Saifullahi Lawal da sunki 230 na hodar Iblis, Daily Trust ta wallafa hakan.

Mukaddashin shugaban hukumar kwastam a jihar Katsina, Dalha Wada-Chedi, ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin mika wanda ake zargin da kayan da aka kama shi hannun hukumar yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA.

Read also

Shugaban NDLEA: Ba kudi a hukumar NDLEA, daga gidana na dauko TV zuwa ofis

Katsina: Jami'an kwastam sun yi ram da matashi dauke da sunki 230 na hodar Iblis
Katsina: Jami'an kwastam sun yi ram da matashi dauke da sunki 230 na hodar Iblis. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

Wada-Chedi, wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban hukumar reshen jihar Katsina, Baffa Dambam, ya ce an kama wanda ake zargin da hodar iblis a wurin garin Shargalle da ke kan babban titin Daura zuwa Katsina a karamar hukumar Mashi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a yayin amsa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa wannan ne karo na uku da ya ke safarar miyagun kwayoyi daga Legas zuwa Katsina ba tare da ya san cewa hodar iblis bace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jama'a na neman mafaka bayan jami'an kwastam sun bude musu wuta kan kisan abokin aikinsu

A wani labari na daban, jami'an hukumar kwastam ta kasa, NCS, sun fada wani kauye da ake kira Fagbohun da ke karamar hukumar Yewa ta jihar Ogun inda suka gigita kauyen.

An zargi fusatattun jami'an kwastam din da banka wa wasu gidaje, babura tare da kakkabe fadar dagacin kauyen kuma suka cafke wasu jama'a, Daily Trust ta wallafa.

Read also

Dakarun Hisbah sun damke karuwai 44, sun kwace kwalaben Barasa 684 a Jigawa

Wannan ya biyo bayan kisan gillar da aka yi wa jami'an kwastam biyu bayan arangamar da suka yi da 'yan sumogal a makon da ya gabata.

Daily Trust ta ruwaito cewa, arangamar ta auku ne a ranar Talata da ta gabata yayin da wani jami'in da ke aiki a Federal Operating Unit (FOU), Ikeja, Legas ya isa kauyen domin aiki.

An tattaro cewa, bayan 'yan sumogal sun hango jami'an sintirin, sun dira kansu kuma aka rasa jami'ai biyu a lamarin.

Source: Legit.ng

Online view pixel