Rahoto: Yadda gobara ta kone mutane 10 tare da lalata miliyoyi a Kano

Rahoto: Yadda gobara ta kone mutane 10 tare da lalata miliyoyi a Kano

  • Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewa akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu sakamakon tashe-tashen gobara da aka samu a jihar a watan Oktoba
  • Kakakin hukumar, Saminu Yusif, ya kuma ce an yi asarar dukiya na kimanin naira miliyan 30 a annobar
  • Sai dai kuma ya ce an yi nasarar ceto mutane 60 da kaya na kimanin naira miliyan 76.7

Jihar Kano - Jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewa akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu sakamakon tashe-tashen gobara da aka samu a jihar.

Hukumar wacce ta bayyana hakan a ranar Talata, 2 ga watan Nuwamba, ta ce wannan ya faru ne a cikin watan Oktoba kacal.

Rahoto: Yadda gobara da kone mutane 10 tare da lalata miliyoyi a Kano
Rahoto: Yadda gobara da kone mutane 10 tare da lalata miliyoyi a Kano Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Saminu Yusif, ne ya bayyana hakan yayin da yake bitar watan Oktoba, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rushewar benen Ikoyi: Yawan mamata ya kai 20, ana kokarin ceto wasu a cikin ginin

Yusuf ya bayyana cewa an ceto jimillar mutane 60 da ransu daga tashe-tashen gobarar da suka faru a cikin watan da ake magana a kai.

Ya kuma ja hankalin jama'a da su kasance masu yin taka-tsan-tsan da abun da ya shafi wuta da kuma guje ma abun da ka iya haddasa hatsari a hanya, rahoton Punch.

A cewarsa:

"Mun samu jimillar kiraye-kiraye na tashin gobara 57, 37 daga ciki sun kasance na neman taimako sannan 13 sun kasance kiran bogi.
"An rasa rayuka 10 sannan an ceto mutane 60.
"An yi asarar kayayyaki da suka kai kimanin naira miliyan 30.7 a gobarar yayin da aka tsiratar da kayayyaki da suka kai kimanin naira miliyan 76.7.
"Muna amfani da wannan damar don shawartar jama'a da su yi taka-tsan-tsan da abun da ya shafi wuta don guje ma annoba, bugu da kari su kasance masu bin dokar hanya don kiyaye hatsarurruka sannan su sanya idanu a kan shige da ficen yara musamman zuwa wuraren rafi yin wanka da sauran wurare masu hatsari."

Kara karanta wannan

Kaduna: Duk da datse layikan sadarwa, 'yan bindiga sun sace mutum 9, sun bukaci N50m

Dinbin mutane sun makale carko-carko yayin da gini mai hawa 20 ya ruguje a Najeriya

A wani labari na daban, mun kawo cewa wani dogon gini ya ruguje a garin Ikoyi, jihar Legas, a kudu maso yammacin Najeriya.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamba, 2021, cewa wannan dogon gini da ke unguwar Ikoyi ya kife dazu da rana.

Rahotanni sun tabbatar mana cewa wannan zungureren gini da yake yankin Alexandria Avenue a unguwar ta Ikoyi ya na da tsawon hawa 20.

Asali: Legit.ng

Online view pixel