Kaduna: Yadda 'yan bindiga suka sace mutum 60 yayin da suke ibada a coci

Kaduna: Yadda 'yan bindiga suka sace mutum 60 yayin da suke ibada a coci

  • Bayan ‘yan bindiga sun isa su na harbe-harbe sun sace a kalla mutane 60 a cocin Emmanuel Baptist da ke Kakau Daji a karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna yayin da su ka je yin bauta ranar Lahadi
  • Shugaban Kungiyar kiristocin Najeriya reshen jihar Kaduna, Reberen John Hayab ya tabbatar wa da manema labarai farmakin inda ya ce abinda ya sa labarin be yadu ba saboda babu kafar sadarwa a yankin ne
  • An samu rahotanni akan yadda su ka yi garkuwa da mutane sun kai 100, sai dai shugaban CAN din ya tabbatar da garkuwa da mutane 60 ne bisa rahoton da mazauna yankin su ka bayar

Jihar Kaduna - A kalla mutane 60 ‘yan bindiga su ka sace a cocin Emmanuel Baptist da ke Kakau Daji a karamar hukumar Chikun a jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Read also

Innalillahi: Yan bindiga sun zagaye wurin Ibada, sun buɗe wa mutane wuta a jihar Kaduna

‘Yan bindigan sun isa cocin dauke da miyagun makamai inda su ka fara harbe-harbe ko ta ina ana tsaka da bautar ranar Lahadi.

Kaduna: Yadda 'yan bindiga suka sace mutum 60 yayin da suke ibada a coci
Yadda 'yan bindiga suka sace mutum 60 yayin da suke ibada a cocin Kaduna. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya ta CAN, reshen jihar Kaduna, Reberen John Hayab ya tabbatar wa da Daily Trust aukuwar farmakin.

A cewarsa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi sai dai ba a samu bayanai akan lokaci ba saboda rashin kafar sadarwa a yankin.

An samu rahotonni akan yadda ‘yan bindigan su ka sace mutane sun kai 100, amma ya tabbatar da satar mutane 60 ne bisa rahoton mazauna kauyen.

A cewarsa:

“Jiya (Litinin), na tabbatar da satar mutane 60 bayan sun je bauta coci da kuma kisan mutum 1. Sun wuni su na bauta ne. Lokacin da ‘yan bindigan su ka isa wurin, bangaren yara su ka fara zuwa sai su ka canja shawara su ka zagaye cocin.”

Read also

Kaduna: Duk da datse layikan sadarwa, 'yan bindiga sun sace mutum 9, sun bukaci N50m

Ya bayyana yadda su ka bude wuta bayan sun ga mutane na gudu dalilin haka su ka halaka wani mutum 1.

Kwamishinan tsaro ma ya tabbatar da harin

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da farmakin inda ya bayyana kisan mutum 1 amma be sanar da satar mutanen da ‘yan bindigan su ka yi ba.

Aruwan ya ce sunan mamacin Yusuf Dauda.

An kashe Dogo Giɗe, ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga da ya daɗe yana addabar jihohin arewa

A baya, Legit ta kawo muku wani rahoto da ya ce an kashe hatsabibin shugaban 'yan bindiga Dogo Gide.

An kashe shi ne a dajin Kuyanbana da ke jihar Kaduna kamar yadda PRNigeria ta wallafa.

A watan Maris na shekarar 2018, Gide ya kashe hatsabibin shugaban yan bindiga a wannan lokacin, Buharin Daji, bayan hakan ne ya zama shugaban yan bindigan yankin.

Source: Legit.ng

Online view pixel