Miyagun yan bindiga sun kai hari dakin bauta a Kaduna, sun bindige mutum 2 sun sace wasu da dama

Miyagun yan bindiga sun kai hari dakin bauta a Kaduna, sun bindige mutum 2 sun sace wasu da dama

  • Miyagun yan bindiga sun harbe mutum biyu, tare da sace wasu da dama a wani sabon hari da suka kai jihar Kaduna
  • Rahoto ya bayyana cewa maharan sun zagaye cocin Baptist a ƙaramar hukumar Chikun, suka buɗe wa masu aikin ibada wuta
  • Kungiyar kiristoci CAN ta bayyana rashin jin daɗinta bisa abinda ta kira kisan kiyashin da akewa mambobinta

Kaduna - Wasu yan bindiga sun kai hari cocin Baptist dake Kakau Daji, karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, inda suka kashe mutum biyu.

This Day tace maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mutane da dama yayin da suke tsaka da gudanar da ayyukan bauta a cocin ranar Lahadi.

Wata majiya ta tabbatar da cewa maharan da suka zo da yawa, sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi bayan sun zagaye cocin baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Kaduna: Duk da datse layikan sadarwa, 'yan bindiga sun sace mutum 9, sun bukaci N50m

Yan bindiga sun.kai sabon hari Kaduna
Miyagun yan bindiga sun kai hari dakin bauta a Kaduna, sun bindige mutum 2 sun sace wasu da dama Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Mutum nawa maharan suka sace?

Shugaban Baptist reshen jihar Kaduna, Ishaya Jangado, ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma yace ba'a san adadin yawan mutanen da suka sace ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Lamarin yafaru da safiyar nan, amma har yanzun bamu san adadin mutanen da suka sace ba."

Shin yan sanda sun samu rahoto?

Da aka tuntubi kakakin yan sandan Kaduna, Mohammad Jalige, ta wayar salula, ba'a same shi ba, domin jin ta bakin yan sanda.

Karamar hukumar Chikun na ɗaya daga cikin yankunan da gwamnati ta datse hanyoyin sadarwa, kuma aka hana amfani da mashin, a wasu matakai na daƙile ayyukan mahara.

CAN ta yi martani

Da yake martani kan lamarin, shugaban ƙungiyar kiristoci (CAN) reshen jihar Kaduna, Joseph Hayab, yace harin da ake kaiwa kwanan nan ya yi muni.

Hayab ya koka cewa yan ta'adda na cigaba da kashe rayukan mutane kamar wasu kaji kuma ba tare da ɗaukar matakai a kansu ba.

Kara karanta wannan

Kogi: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 6, sun babbaka fadar Sarki da wasu gidaje masu yawa

The cable ta rahoto Hayab yace:

"Waɗan nan mutanen sun jima suna cutar da mu, ina miƙa ta'aziyya ta ga yan Baptist da kuma sauran kiristocin jihar Kaduna bisa wannan rashi."

A wani labarin kuma Dalilin da yasa har yanzun Gwamnatin Buhari ba ta ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda ba

Ministan tsaron ƙasar nan, Bashir Magashi, ya bayyana cewa bahakanan kawai gwamnati zata fito ta ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda ba.

Ministan yace akwai matakai da ya zama wajibi gwamnati ta bi kafin ɗaukar wannan matakin, kuma a yanzun an kusa kammala wa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel