‘Yan bindiga sun kashe wani dan bangan da suka sace bayan sun karbi kudin fansa naira miliyan biyu

‘Yan bindiga sun kashe wani dan bangan da suka sace bayan sun karbi kudin fansa naira miliyan biyu

  • Masu garkuwa da mutane sun halaka wani dan banga da suka sace bayan sun karbi kudin fansa
  • 'Yan uwan mamacin sun kukuta sun hada naira miliyan biyu domin karbar fansarsa amma kuma sai maharan suka kashe shi a wajen bayan sun karbe kudin
  • Sai dai kuma, kakakin 'yan sandan jihar Nasarawa, ASP Ramhan Nansele, ya ce rundunar ta san batun sace shi ne kawai

Nasarawa - 'Yan bindiga sun kashe wani dan banga da suka yi garkuwa da shi mai suna Ohikwo bayan yan uwansa sun biya naira miliyan biyu a matsayin kudin fansarsa.

Daily Trust ta rahoto cewa an yi garkuwa da dan bangan ne a yankin Toto da ke jihar Nasarawa yayin da yake komawa kauyensa na Atako kimanin makonni uku da suka gabata.

Read also

Da Dumi: An tsinci gawar ƴan bindiga 3 da suka kashe kansu wurin faɗan rabon kuɗin fansa a wata jihar Arewa

‘Yan bindiga sun kashe wani dan bangan da suka sace bayan sun karbi kudin fansa naira miliyan biyu
‘Yan bindiga sun kashe wani dan bangan da suka sace bayan sun karbi kudin fansa naira miliyan biyu Hoto: Daily Trust
Source: UGC

Wani dan uwan marigayin wanda ya tabbatar da lamarin, ya fada ma jaridar cewa iyalan sun yi cuku-cuku sun hada naira miliyan biyu domin biyan fansarsa amma duk da haka sai da wadanda suka yi garkuwa da shi suka kashe shi.

Ya ce sun kashe shi ne bayan sun karbi kudin saboda sun gano cewa shi dan kungiyar 'yan banga ne.

Ya ce:

"An kashe Ohikwo a wajen da suka nemi a kai kudin fansar. mutumin da ya kai kudin fansar ya dawo yana kuka kan kisan."

Kakakin 'yan sandan jihar Nasarawa, ASP Ramhan Nansele, ya ce rundunar ta san batun sace shi ne kawai.

Masu garkuwa da mutane sun sace babban limami da 'ya'yansa 2 a Abuja

A wani labari kuma, babban limamin masallacin Yangoji da ke yankin Kwali a Abuja, Abdullahi Abubakar Gbedako mai shekaru 59 tare da 'ya'yansa biyu, Aliyu Usman Abubakar mai shekaru 22 da Ibrahim Abubakar mai shekaru 11 sun shiga hannun masu garkuwa da mutane.

Read also

Dogo Giɗe, hatsabibi shugaban ƴan bindiga ya haramta shan giya da kayan maye a wasu ƙauyukan Zamfara

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, wani makwabcinsu mai suna Shuaibu, ya ce lamarin ya auku a daren Juma'a wurin karfe 11:47 na yamma yayin da aka sace shi. Sun bayyana da yawansu dauke da makamai sannan suka kutsa gidan babban limamin.

Ya ce wasu daga cikin 'yan bindigan sun tsaya a wurare daban-daban inda suka dinga harbi a iska yayin da wasu uku suka tsallake katangar gidan limamin.

Source: Legit.ng

Online view pixel