Buhari ya shiga jimami, ya mika sakon jaje ga iyalan wadanda bene ya ruguje dasu

Buhari ya shiga jimami, ya mika sakon jaje ga iyalan wadanda bene ya ruguje dasu

  • Jim kadan bayan rugujewar wani bene a jihar Legas, Shugaba Buhari ya mika sakon jaje
  • Ya bayyana bakin cikinsa ga rashin da aka yi, inda ya nemi cibiyoyin agajin gaggawa su taimaka a ceto rayuka
  • Shugaban ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar ranar Talata 2 ga watan Nuwamba

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya mika sakon jaje ga iyalan wadanda rugujewar bene mai hawa 22 ya rutsa dasu a jihar Legas ranar Litinin.

A ranar Litinin 1 ga watan Nuwamba ne wani bene mai hawa 22 ya ruguje, inda mutane suka halaka wasu kuma aka yi nasarar ceto su da munanan raunuka.

Da yake bayyana jimaminsa, Shugaba Buhari ya bayyana bukatar daukar matakin gaggawa wajen ceto rayukan wadanda aka ciro daga cikin ginin.

Kara karanta wannan

So makaho: Matashi ya fada soyayyar 'yar fim da ta girme shi, ya daina cin abinci saboda begenta

Buhari ya shiga jimami, ya mika sakon jaje ga iyalan wadanda bene ya ruguje dasu
Shugaba Buhari na Najeriya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren yada labarai, Femi Adesina ya fitar a shafin Facebook.

A cewar sanarwar:

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu a wani bene mai hawa 22 da ya ruguje a Legas, yayin da wasu ke makale har yanzu.
"Shugaba Buhari ya bayyana bakin cikinsa ga jama’a da gwamnatin jihar Legas, inda ya bukaci hukumomi su kara kaimi wajen gudanar da ayyukan ceto, yayin da ya bukaci cibiyoyin agajin gaggawa ciki har da asibitoci su ba da duk wani tallafi da ya dace domin kare rayukan wadanda aka ceto.
"Shugaban ya yi addu’ar Allah ya taimaka a aikin da ake na ceto a halin yanzu."

An fara zaro gawarwakin mutane daga gini mai hawa 21 da ya rushe a Najeriya

Kara karanta wannan

Bincika Gaskiya: Shin hukumar 'yan sanda ta dawo da Abba Kyari bakin aiki bayan bincike?

A wani labarin, jaridar Dailytrust ta rahoto cewa aƙalla gawar mutum uku aka gano zuwa yanzun daga ɓaraguzan gini mai hawa 21 da ya rushe a jihar Legas ranar Litinin.

Babban ginin, wanda ake cikin ginawa, ya ruguje ne a kan hanyar Gerald dake yankin Anguwar highbrow a jihar Legas.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa, NEMA, Ibrahim Farinloye, yace an matsar da gawarwakin zuwa ɗakin ajiye gawa mallakin gwamnatin jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel