Da Dumi-Dumi: An fara zaro gawarwakin mutane daga gini mai hawa 21 da ya rushe a Najeriya

Da Dumi-Dumi: An fara zaro gawarwakin mutane daga gini mai hawa 21 da ya rushe a Najeriya

  • Jami'an hukumar agaji NEMA sun samu nasarar gano gawar mutum uku daga cikin dogon ginin da ya rushe a jihar Legas
  • Hakanan an kuma ceto wasu mutum uku da suke da sauran numfashi a gaba, suna asibiti ana kulawa da lafiyarsu
  • Wani dogon gini da ba'a kammala ba ya ruguje kan mutane a ƙan hanyar Gerald dake Anguwar highbrow, jihar Legas

Lagos - Jaridar Dailytrust ta rahoto cewa aƙalla gawar mutum uku aka gano zuwa yanzun daga ɓaraguzan gini mai hawa 21 da ya rushe a jihar Legas ranar Litinin.

Babban ginin, wanda ake cikin ginawa, ya ruguje ne a kan hanyar Gerald dake yankin Anguwar highbrow a jihar Legas.

Ginin da ya rushe a Legas
Da Dumi-Dumi: An fara zaro gawarwakin mutane daga gini mai hawa 21 da ya rushe a Najeriya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa, NEMA, Ibrahim Farinloye, yace an matsar da gawarwakin zuwa ɗakin ajiye gawa mallakin gwamnatin jihar Leagas.

Kara karanta wannan

Bayan tsige shi, 'yan sanda sun kame shugaban majalisar dokokin Filato da tawagarsa

Mista Farinloye yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Jami'ai sun gano gawarwakin ne daga ƙarƙashin wasu ɓaraguzan ginin da ya rushe."

Shin an gano wasu da rai?

Hukumomi sun tabbatar da cewa an samu nasarar ceto wasu mutum uku da ransu, kuma yanzu haka suna asibiti ana kula da lafiyarsu.

PM News ta rahoto ragujewar ginin a ranar Litinin, amma tace har yanzu da ake tattara labarin, babu cikakken labari game da yanayin da ake ciki.

Matasa sun mamaye majalisar Filato

A wani labarin na daban kuma Zanga-Zangar Matasa a majalisar dokokin Filato ta dauki sabon salo, An fara harbe-harbe

A halin yanzun wasu matasa da ake tsammanin magoya bayan sabon kakakin majalisa ne, Yakubu Sanda, sun kutsa kai cikin zauren ta kofar baya.

Hakan ya harzuƙa magoya bayan tsohon kakaki, amma jami'an tsaro suka fara harbi a iska domin kwantar da tarzomar.

Kara karanta wannan

Dinbin mutane sun makale carko-carko yayin da gini mai hawa 20 ya ruguje a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: