Da duminsa: Yan bindiga sun kai hari Jami'ar Abuja SQ, sun kwashe ma'aikata da 'yayansu

Da duminsa: Yan bindiga sun kai hari Jami'ar Abuja SQ, sun kwashe ma'aikata da 'yayansu

  • Cikin dare, yan bindiga sun afka Jami'ar birnin tarayya Abuja inda suka kwashe mutane da dama
  • Hukumomi a jami'ar sun bayyana cewa an zuba jami'an tsaro su bibiyi yan bindigan don ceto wadanda aka sace
  • Wannan shine karo na farko da irin wannan mumunan abu ke faruwa da jami'ar ta birnin tarayya

Gwagwalada - Wasu tsagerun yan bindiga sun kai hari gidajen Malaman jami'ar Abuja (UniAbuja) cikin daren Talata, 2 ga watan Nuwamba 2021 kuma sun yi awon gaba da mutane.

Legit Hausa ta tattaro cewa yan bindiga sun dira gidajen ne dake unguwar Giri, hanyar zuwa tashar jirgin sama Gwagwalada, Abuja.

An sace wani Farfesa Oboskolo, wanda ke tsangayar Ilimi a jami'ar.

Hakazalika Jami'ar ta bayyana cewa tuni an tura jami'an tsaro domin tabbatar da tsaro a wajen.

Jami'ar ta sanar da wannan hari a shafinta na Facebook.

Tace:

"Wasu yan bindiga sun kai hari gidajen ma'aikatan jami'ar Abuja da safiyar nan. Tuni mun tura jami'an tsaro domin kare mutane."

Yan bindiga sun kai hari Jami'ar Abuja
Da duminsa: Yan bindiga sun kai hari Jami'ar Abuja SQ, sun kwashe ma'aikata da 'yayansu Hoto: University of Abuja
Asali: Facebook

Mutum nawa aka sace?

Jami'ar ta bayyana cewa an yi awon gaba da ma'aikatan jami'ar akalla mutum hudu da iyalansu.

"Muna sanar da cewa an sace ma'aikatanmu hudu da yaransu. Muna kokarin tabbatar da cewa sun kubuta. Yau dai ba dadi," jawabin ya kara.

Legit ta tattauna da wasu Malamai da Mazauna wajen

A hirar da Legit Hausa tayi da wata Farfesa, ta bayyana mana cewa lallai an yi awon gaba da abokan aikinsu.

Dan wani Farfesa a tsangayar Lissafi, Yinka Rafiu, ya bayyana ma wakilin Legit cewa Farfesa daya aka sace tare da yaransa.

A cewarsa, da farko an sace matarsa amma daga baya aka sake ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel