Da dumi-dumi: Hawaye sun kwaranya yayin da Najeriya ta sake rashi na wani tsohon sanata

Da dumi-dumi: Hawaye sun kwaranya yayin da Najeriya ta sake rashi na wani tsohon sanata

  • Tsohon dan majalisa wanda ya wakilci yankin Ondo ta Kudu a majalisar dattawa, Sanata Hosea Ehinlanwo ya rasu
  • Ehinlanwo ya rasu ne a gidansa da ke babbar birnin tarayya Abuja bayan ya yi fama da yar gajeriyar rashin lafiya
  • Marigayin ya amsa kiran Allah yana da shekaru 83 a duniya

Abuja - Allah ya yiwa shahararren dan siyasan Najeriya kuma tsohon sanatan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Sanata Hosea Ehinlanwo rasuwa, Sahara Reporters ta rahoto.

Tsohon dan majalisar wanda ya wakilci yankin Ondo ta Kudu a majalisar dattawa tsakanin 2003 da 2011 ya mutu a gidansa da ke Abuja bayan yar gajeriyar rashin lafiya, jaridar The Nation ta kuma rahoto.

Da dumi-dumi: Hawaye sun kwaranya yayin da Najeriya ta sake rashi na wani tsohon sanata
Da dumi-dumi: Hawaye sun kwaranya yayin da Najeriya ta sake rashi na wani tsohon sanata Hoto: The Nation
Asali: UGC

Dan marigayin mai suna Soji ne ya tabbatar da hakan. Kuma mahaifin nasa ya rasu yana da shekaru 83.

Kara karanta wannan

Fitattun 'yan Najeriya 5 da ke jan ragamar shugabancin wasu manyan hukumomin duniya

Marigayin wanda ya kasance lauya kuma tsohon kansila, ya kasance hadimin tsohon ministan sadarwa, marigayi Cif Olu Akinfosile.

Ya koyar a kwalejin Lagas, Sabo, jihar Lagas da kuma sashin kasuwanci, jami’ar Olabisi Onabanjo, Ago-Iwoye, jihar Ogun.

Ya yi aiki a kamfanin kiwon kifi, inda ya kai mukamin mataimakin babban manaja kafin ya bar wajen a 1979. Lokacin da aka kafa kamfanin Oluwa Glass Limited, sai ya zama manaja sannan daga bisani aka nada shi a matsayin sakataren hukumar.

Yana da hannu wajen kafa bankin Ese-odo inda ya kasance babban ciyaman.

Yayin da yake a majalisar dattawa, ya kasance shugaban kwamitin majalisar kan kidaya da katin shaidar dan kasa da kuma kwamitin sojin ruwa.

Ya kuma kasance mamba a kwamitin da’a da kuma kwamitin rundunar soji, man fetur da kuma kwamitin gyara kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Andy Uba boyi-boyin Obasanjo ne a cikin gida, mai goge masa takalma ne, Soludo

Ya kasance Baba Ijo na cocin C&S har zuwa mutuwarsa.

‘Yan bindiga sun mamaye gidan rasuwa, sun sace bakin da suka halarci jana’iza

A wani labari na daban, wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a yammacin ranar Talata sun yi garkuwa da wasu mutane takwas da suka halarci jana’iza a Itapaji-Ekiti da ke karamar hukumar Ikole a jihar Ekiti.

Lamarin ya faru ne mako guda bayan da aka yi garkuwa da mutane hudu a Ayebode-Ekiti a karamar hukumar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun yiwa wani gida kawanya da ke tsakiyar garin da misalin karfe 9:30 na dare inda suka yi ta harbe-harben iska kafin su yi awon gaba da mutane 14 da ke cikinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel