Andy Uba boyi-boyin Obasanjo ne a cikin gida, mai goge masa takalma ne, Soludo

Andy Uba boyi-boyin Obasanjo ne a cikin gida, mai goge masa takalma ne, Soludo

  • Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Charles Soludo, ya ce Andy Uba tsohon boyi-boyi ne a baya
  • Soludo ya ce Uba har goge takalmin Obasanjo ya ke a baya kuma ba shi da shaidar kammala karatu
  • Kamar yadda Soludo ya bayyana, abokin adawarsa ya mika takardun bogi ne ga INEC don haka zai fallasa shi

Chukwuma Soludo, dan takarar kujerar gwamna a jihar Anambra karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), ya ce Andy Uba, dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ma'aikacin cikin gida ne na tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Soludo ya sanar da hakan a ranar Litinin yayin da aka yi muhawara tsakanin 'yan takarar gwamnan jihar Anambra wanda Arise TV ta shirya.

Andy Uba boyi-boyin Obasanjo ne a cikin gida, mai goge masa takalma ne, Soludo
Andy Uba boyi-boyin Obasanjo ne a cikin gida, mai goge masa takalma ne, Soludo. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Yayin muhawarar, Soludo da Uba sun dinga jifan juna da zargi daban-daban, The Cable ta wallafa.

Kara karanta wannan

Bayan lashe zabe, sabon shugaban matasan PDP ya magantu kan manufarsa akan APC

A jawabinsa, Soludo ya yi ikirarin cewa Uba bai yi wa jama'arsa aikin komai ba yayin da ya ke sanata.

A yayin martani, Uba ya ce ya kira sunan Soludo ne yayin da ya ke gwamnan babban bankin Najeriya karkashin Obasanjo.

"Ka na cewa a cikin shekaru takwas da nayi a majalisa, ban yi komai ba. Kai ne ka yi? A lokacin da ka ke gwamnan babban banki, me ka yi?" dan takarar APC ya tambaya.
"Ba ka yi komai ba. An kawo ka gaba na. Dan uwana ya kawo ka. Ya za ka ce ba ka sani ba?"

A martanin Uba, tsohon gwamnan babban bankin ya yi ikirarin cewa abokin hamayyarsa ya mallaki shaidar kammala sakandare ta bogi wacce ya mika gaban hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC.

Kara karanta wannan

Rade-Radin sauya sheka zuwa APC: An gano babban dalilin da ya hana Goodluck Jonathan halartan gangamin PDP

"Ba ka da kwalin makaranta. Na bogi gare ka. Za mu fallasa ka a nan. Ka na da shaidar sakandare?" Soludo ya tambaya.
“Yaushe ka kammala jami'a? Ka samu shaidar kammala sakandare a 1974? Ka yi SSCE a Enugu ko? Duk na bogi ne! Tarihin ka nan nan. Zan iya nuna maka daga INEC."

A yayin martani ga tsokacin Uba kan aikinsa na CBN, Soludo ya ce Andy Uba ba shi da hannu a zamansa gwamnan CBN, ya kara da cewa Uba dan aiki ne a fadar shugaban kasa.

"Na san Andy mai yin tausa ne Amurka. Dan aiki ne a fadar shugaban kasa wanda ke goge takalman shugaban kasa," yace.

Soludo ya magantu kan tsame sunansa daga na 'yan takara a Anambra

A wani labari na daban, Chukwuma Soludo, daya daga cikin 'yan takarar zaben gwamnonin da za a yi a jihar Anambra na ranar shida ga watan Nuwamban shekarar nan yace har yanzu yana cikin 'yan takara.

Kara karanta wannan

Taron gangamin PDP: Ba zan yarda ba, zan tafi kotun koli - Uche Secondus

Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta cire sunan shi daga cikin jerin 'yan takara.

A wata takarda da kungiyar yakin neman zabensa ta fitar a madadinsa, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ya ce har yanzu shine dan takarar jam'iyyar APGA, Daily Trust ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel