‘Yan bindiga sun mamaye gidan rasuwa, sun sace bakin da suka halarci jana’iza

‘Yan bindiga sun mamaye gidan rasuwa, sun sace bakin da suka halarci jana’iza

  • Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari gidan mutuwa, inda suka sace mutane da yawa cikin baki
  • An ce, ana shirin binne gawar wata mata ne lokacin da 'yan bindigan suka shigo suka kwantar da kowa a gidan
  • Rundunar 'yan sandan jihar Ekiti ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana fara bincike a kan lamarin

Ekiti - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a yammacin ranar Talata sun yi garkuwa da wasu mutane takwas da suka halarci jana’iza a Itapaji-Ekiti da ke karamar hukumar Ikole a jihar Ekiti.

Lamarin ya faru ne mako guda bayan da aka yi garkuwa da mutane hudu a Ayebode-Ekiti a karamar hukumar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun yiwa wani gida kawanya da ke tsakiyar garin da misalin karfe 9:30 na dare inda suka yi ta harbe-harben iska kafin su yi awon gaba da mutane 14 da ke cikinsa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana alherin da katse hanyoyin sadarwa ya jawo

‘Yan bindiga sun mamaye gidan rasuwa, sun sace bakin da suka halarci jana’iza
Miyagun 'yan bindiga | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

A cewar wani ganau, harbe-harbe da aka kwashe sama da sa’a daya da rabi an ce ya tsoratar da daukacin al’ummar yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta bayyana cewa mai gidan yana shirye-shiryen binne mahaifiyarsa ne a lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari.

Shaidan ya kuma bayyana cewa, maharan sun zo ne su bakwai da misalin karfe 9:30 na dare.

Ya kara da cewa:

“Da safiyar yau (Laraba), daya daga cikin ‘yan uwa ya samu kira daga wadanda suka yi garkuwar inda suka bukaci a biya su kudin fansa N50m.”

Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ekiti, Sunday Abutu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa Kwamishinan ‘yan sanda, Tunde Mobayo, ya umarci jami'ansa da su fara neman wadanda aka sacen.

A kalamansa:

“Hukumar tana aiki akan hakan. Tuni aka tura jami’an ‘yan sanda na musamman da kuma JTF a wannan sashe domin tabbatar da ceto wadanda abin ya shafa da kuma yiyuwar cafke masu laifin.”

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Ana ci gaba da samun hare-haren 'yan bindiga a yankuna daban-daban na Najeriya, duk da cewa rundunonin tsaro na kokarin dakile 'yan bindiga.

A kwanan nan ne wasu 'yan bindiga suka kai hari kan wasu masallata a jihar Neja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Sabon hari: 'Yan bindiga sun hari ofishin 'yan sanda, sun kashe 3, an hallaka dan bindiga 1

A wani labarin, The Nation ta ruwaito cewa, an harbe jami’ai uku a cikin ofishin ‘yan sanda da ke Unwana, karamar hukumar Afikpo ta Arewa a jihar Ebonyi.

Wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa jami’an da suka mutu akwai kwanstabul da sifetoci biyu.

Wani mazaunin Uwana, wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya ce 'yan bindigar sun rufe fuska.

Asali: Legit.ng

Online view pixel