Yanzu-yanzu: An tsinci gawar jami'in kwastam da miyagu suka yi garkuwa da shi

Yanzu-yanzu: An tsinci gawar jami'in kwastam da miyagu suka yi garkuwa da shi

  • Jami'ai sun tsinta gawar 1 daga cikin jami'an hukumar kwastam wanda wasu 'yan sumogal suka sace a ranar Talata
  • Jami'an suna tsaka da sintiri a Yewa ta kudu, ashe miyagun sun yi musu kwanton bauna, kwatsam suka bude musu wuta
  • An tsinta gawar ne kusa da rafin kauyen Fagbohun da ke jihar Ogun bayan ganin bindigar jami'in da aka yi

Ogun - An tsinci gawar jami'in hukumar kwastam da ake sace a jihar Ogun a ranar Talata da ta gabata, Daily Trust ta wallafa.

Wasu miyagu da ake zargin 'yan sumogal ne suka yi wa jami'an kwanton bauna yayin da suka fita sintiri a karamar hukumar Yewa ta kudu da ke jihar kuma suka sace jami'ai biyu.

Yanzu-yanzu: An tsinci gawa jami'in kwastam da miyagu suka yi garkuwa da shi
Yanzu-yanzu: An tsinci gawa jami'in kwastam da miyagu suka yi garkuwa da shi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An tsinta gawar daya daga cikin jami'an a wani rafi kusa da kauyen Fagbohun da ke karamar hukumar a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Osinbajo da Tinubu sun hadu ana tsaka da rade-radin baraka a tsakaninsu

Bayan sa'o'in da aka kwashe ana nemansa, an fara ganin bindigarsa kuma daga bisani aka ga gawarsa mitoci kadan kusa da rafin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'an da ke aiki da Legas da Ogun ne suka fita sintiri a yankin ranar Talata da rana inda aka sace jami'an biyu, Daily Trust ta wallafa.

A yayin jawabi ga manema labarai kan farmakin, shugaban jami'an na yankin shiya ta A da ke Ikeja, Hussein Kehinde Ejibunu, ya ce a ranar 16 ga watan Oktoba ne wasu 'yan sumogal suka kai wa jami'an farmaki.

Shugaban kwastam na shiyar ya ce jami'an sun ga ababen hawa 24 dauke da shinkafa da kuma motoci 12 da jami'an suka kai hedkwatarsu da ke Legas.

'Yan sanda sun samo gawar basaraken da aka yi garkuwa da shi

A wani labari na daban, Rundunar 'yan sandan jihar Ribas ta samo gawar basarake mai shekaru sittin da daya wanda aka sace a shekarar 2019.

Kara karanta wannan

Dogo Giɗe, hatsabibi shugaban ƴan bindiga ya haramta shan giya da kayan maye a wasu ƙauyukan Zamfara

Jami'an 'yan sanda sun samo gawar Chief Robert Loolo ne a wasu yankuna da suka hada garuruwan Luwa, Bera da Bane, Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa, har gida wasu matasa suka je inda suka tasa keyar Loolo a ranar 27 ga watan Yunin 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel