Kungiyar Arewa ga gwamnatin Buhari: Ku fallasa masu daukar nauyin 'yan ta'adda a kasar nan

Kungiyar Arewa ga gwamnatin Buhari: Ku fallasa masu daukar nauyin 'yan ta'adda a kasar nan

  • Wata kungiyar 'yan Arewa ta bukaci gwamnatin Buhari ta gaggauta fallasa masu daukar nauyin 'yan ta'adda
  • Ta kuma bukaci gwamnatin ta kara kaimi wajen yaki da ta'addanci da suka addabi Najeriya a yanzu
  • Ta bayyana haka ne a Kaduna yayin taron karrama shugaban kungiyar, marigayi Alhaji Isiaq Sanni

Kaduna - Daily Trust ta ruwaito cewa, Majalisar Jihohin Arewa ta Ansar-ud-Deen Society of Nigeria, ta bukaci Gwamnatin Buhari da ta tona asirin masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci da masu 'yan ta'adda a Najeriya.

Sakataren kungiyar, Alhaji Isiaq Sanni ne ya yi wannan kiran a Kaduna lokacin da kungiyar da al’ummar Yarbawa suka karrama shugabansu marigayi Alhaji Liadi Adeyinka Olapade.

Kungiyar Arewa ga gwamnatin Buhari: Ku fallasa masu daukar nauyin 'yan ta'adda a kasar nan
'Yan bindiga a Najeriya | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Da yake jawabi a wajen taron addu’o’in Fidau na kwana 8 da aka shirya domin karrama marigayi Alhaji Olapade, Sakataren kungiyar Ansar-ud-Deen ya ce marigayin ya rayu, ya yi aiki kuma ya mutu a kan fafutukar ganin an samu hadin kai da tabbatar da Najeriya ta hanyar bunkasa ilimin ‘yan kasa.

Kara karanta wannan

2023: CAN ta yi gargaɗi kan tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimaki masu addini iri ɗaya

A cewar Sanni:

“Alhaji Liadi Olapade ya kasance mai taimakon jama’a, kadan daga abubuwan da muka gani sun nuna cewa ana kaunarsa sosai. Ya yi matukar kyautatawa al'ummar Ansar-ud-Deen da kuma bil'adama baki daya.
“Saboda kishinsa na addini da ilimin ‘yan kasa, wanda yake cewa ita ce hanya mafi dacewa ta yaki da rashin tsaro, ya amince da nadi kuma ya wakilci Majalisar Ansar-ud-Deen ta jihohin Arewa da kyau a hukumar gudanarwar jami’ar mu. Jami'ar Summit.
“Abin takaici ne cewa a yau, rashin tsaro da Olapade ya yi yaki dashi ya ci gaba da wanzuwa. Don haka muna kira ga gwamnati da ta kara himma wajen yakar ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro, domin kokarin da suke yi a halin yanzu bai isa a magance kalubalen ba.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun manta Allah: Buhari ya bayyana mafita ga matsalolin Najeriya

"Gwamnati ta gaya mana masu laifin fashi da makami, masu daukar nauyin rashin tsaro, su sanar da mu wadanda ba sa son kasarmu ta ci gaba, wadanda ba sa son gwamnati."

Kungiyoyi da daidaikun mutane a Najeriya na ci gaba da ga gwamnatin Buhari da ta bayyana sunayen masu daukar nauyin ta'addanci a Najeriya.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, jam'iyyar adawa ta PDP ta bukaci gwamnatin Buhari da ta gaggauta fallasa masu daukar nauyin ta'addanci.

PDP ta zargi gwamnatin Buhari da ba 'yan ta'adda da masu daukar nauyinsu kariya kasancewar ta ki bayyana sunyensu.

'Yan bindiga sun yi barna a gidan rasuwa

A wani labarin, Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a yammacin ranar Talata sun yi garkuwa da wasu mutane takwas da suka halarci jana’iza a Itapaji-Ekiti da ke karamar hukumar Ikole a jihar Ekiti.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun tafi kotu, sun bukaci a raba Najeriya, a ware 'yan wani yankin kudu

Lamarin ya faru ne mako guda bayan da aka yi garkuwa da mutane hudu a Ayebode-Ekiti a karamar hukumar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun yiwa wani gida kawanya da ke tsakiyar garin da misalin karfe 9:30 na dare inda suka yi ta harbe-harben iska kafin su yi awon gaba da mutane 14 da ke cikinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel