'Yan sanda sun musanta labarin halaka jami'an tsaro 20 da aka yi a Zamfara

'Yan sanda sun musanta labarin halaka jami'an tsaro 20 da aka yi a Zamfara

  • Rundunar 'yan sanda a jihar Zamfara ta karyata labaran da ke yawo na cewa 'yan bindiga sun halaka jami'ai 20
  • Da farko labarai sun fara yawo na yadda 'yan bindiga suka sheke jami'ai 20 a kan babban titin Kauran Namoda zuwa Shinkafi
  • Kamar yadda kakakin rundunar ya sanar, sun rasa rayukan dan sanda 1 ne da jami'an NSCDC guda 2 a karon da suka yi da 'yan bindiga

Zamfara - Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara a ranar Asabar ta musanta labaran da ake yadawa na cewa kusan jami'an tsaro 20 ne 'yan bindiga suka halaka a kan titin Shinkafi.

Rahotanni a baya sun bayyana cewa, kungiyar 'yan bindigan da suka samu jagorancin Turji, sun kai farmaki kan jami'an tsaro wadanda jami'an NSCDC suka fi yawa da 'yan sa kai, Channels TV ta wallafa.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: An tsinci gawar jami'in kwastam da miyagu suka yi garkuwa da shi

'Yan sanda sun musanta labarin halaka jami'an tsaro 20 da aka yi a Zamfara
'Yan sanda sun musanta labarin halaka jami'an tsaro 20 da aka yi a Zamfara. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

A wata takarda da kakakin rundunar, Mohammed Shehu ya fitar, ya ce rundunar ta tabbatar da farmakin amma ya ce dan sanda 1 da jami'in NSCDS daya kadai suka rasa rayukansu.

"Abinda ya faru shi ne, a ranar 28 ga watan Oktoba, rundunar hadin guiwa ta jami'an 'yan sanda da NSCDC da aka aika titin Kauran Namoda zuwa Shinkafi, sun fada wa 'yan bindigan da suka bayyana da yawansu," takardar tace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa:

"Jami'an tsaron da ke shirye sun yi musayar wuta da miyagun na tsawon sa'o'i. Wasu daga cikinsu an kashe su yayin da wasu suka tsere da raunikan bindiga.
"Sai dai kuma, an rasa rayukan dan sanda 1 da jami'an NSCDC 2 kuma an kwashe gawarwakinsu domin birnesu.
"Kwamishinan 'yan sanda yayin aikewa da jami'an tsaro, ya jaddada cewa za a cigaba da matsantawa 'yan ta'adda tare da tabbatar da cewa an kawar da dukkan miyagu daga jihar."

Kara karanta wannan

Kogi: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 6, sun babbaka fadar Sarki da wasu gidaje masu yawa

Channels TV ta wallafa cewa, rundunar na kira ga jama'a da su yi burus da masu yada rahotannin cewa jami'an tsaro masu yawa ne suka rasa rayukansu kuma su cigaba da al'amuransu.

An bindige Damina, dan bindigan da ya kona mata da ran ta a Zamfara

A wani labari na daban, Damina, wani gagararren dan bindiga kuma shugaban barayin shanu a jihar Zamfara, an bindige shi har lahira.

Mamacin wanda ke da sansani a dajin Kuyanbana da ke masarautar Dansadau a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, ya taba kona wata mata da ran ta yayin daya daga cikin farmakin da ya kai.

An kashe Damina ne sakamakon wata arangama da yayi da kungiyar 'yan bindigan da Dogo Gide ke shugabanta. Daily Trust ta tattaro cewa, mamacin dan bindigan ne ke da alhakin wasu miyagun farmaki, satar mutane, satar shanu da kuma kallafa wa jama'ar yankunan haraji a Dansadau da ke jihar.

Kara karanta wannan

Katsina: Jami'an tsaro sun kai samame sansanonin 'yan bindiga, sun kwato dabbobi 102

Asali: Legit.ng

Online view pixel